MU SAN ANNABINMU (10)

Da Sunan Allah Masanin fili da boye, Salati da aminci su tabbata ga Ma'abocin Alqur'ani da Sab'ul Mathaniy, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da matayensa da dukkan Sahabbansa da Salihan bayin Allah baki dayansu.

AURENSA DA NANA KHADIJAH (RA).

Manzonmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) tyn tasowarsa ya shahara da kyawawan halaye da dabi'u irin su gaskiya da rikon amana da hakuri da kyautatawa, da dukkan wasu halayen ababen yabawa.

Ita kuma Nana Khadijah bintu Khuwailid (ra) wata Mace ce Ma'abociyar kyawu da daukakar nasaba ga kuma dukiya mai yawa wacce Allah ya bata a hannunta. Ta kasance tana bayarwa ana yi mata kasuwanci da dukiyarta ta hanyar aika Mazaje zuwa garuruwa masu nisa domin saye da sayarwa sannan a raba ribar da aka samu.

To Nana Khadijah watarana ta gani acikin mafarkinta cewa rana ta sauko daga sama ta fa'do acikin dakinta, akan Qirjinta. Yayin da ta farka afirgice ta gaya ma wani Malami makarancin Attaura kuma 'Dan Baffanta mai suna Waraqah bn Naufal, sai ya fassara mata da cewa wannan Mafarkin nata bushara ce dake nuna cewa zata auri wani mutum wanda shine zai zamanto Annabin Qarshe daga cikin jerin Annabawan Allah. Kuma shine Mafificinsu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

To lokacin da Shekarun Manzon Allah (saww) suka kai Ashirin da Biyar sai baffansa Abu Talib ya nema masa izini wajen Nana Khadijah (ra) cewa yana son shiga cikin jerin Jama'arta da take turawa domin yin kasuwanci da dukiyarta.

Ta bashi dukiyarta ya tafi zuwa yankin Qasar Sham tare da wani yaronta mai suna Maisarah domin ya rika lura da yanayin Manzon Allah (saww).

Yayin da suka dawo sai shi Maisarah ya bata labarin abinda ya gani na kyawun halin Manzon Allah (saww) da farin jininsa acikin jama'a duk wanda ya ganshi sai ya soshi,  da kuma yadda hannunsa yake da albarka kasancewar sai da ribarsu ta ninninka yadda suke tsammani.

Wannan ya sanya Khadijah (ra) ta Qara sonshi har ta tura wata Qawarta mai suna Nafeesah bintu Munabbih domin ta sanar mishi cewa ita Khadijah din tana sonshi da aure.

Daga nan sai Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya amince kuma yaje tare da Baffaninsa ya nemi aurenta awajen dangin Mahaifinta kuma suka amince.

SADAKIN NANA KHADIJAH (RTA)
*****************
Da ranar daurin aure tazo sai Annabi (saww) yaje tare da baffaninsa, Kuma Abu Talib ya mike yayi kirari tare da godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa ni'imar da yayi musu su Larabawa Quraishawa, Musamman Hashimawa. Sannan ya bayyana kyawawan halaye da fifikon da Annabi Muhammadu (saww) ke dashi atsakanin jama'arsu.

Daga nan sai aka daura aure bisa sadaqin Zinare 'Uqiyah goma sha biyu da rabi. Daga nan sai Nana Khadijah ta tare agidansa (saww).

Ta kasance tana daga cikin mafiya kyawun matayen Quraishawa, Kuma mafi daukakar nasaba da dukiya da ado. Kuma alokacin nan ita bazawara ce 'Yar shekaru Arba'in (40) aduniya. Shi kuma alokacin nan yana da shekaru 25 (ashirin da biyar) aduniya.

Nana Khadijah ta kasance tun azamanin jahiliyyah ana yi mata laqabi da "Tahirah" (Mai Tsarki) saboda kyawawan halayenta da tsaftar jikinta. Kuma kafin Manzon Allah (saww) ta auri mazaje guda biyu kamar haka :

- Abu Halah bn Zurarah At-Tameemi.

- 'Ateequ bn Abid Al Makhzumiy.

Ya Allah kayi salati da aminci bisa Annabinka Muhammadu acikin halittun farko da na Karshe. Ka sanya salatinmu gareshi ya zamto kariya garemu daga kowanne abun Qi aduniya da lahira ameen.

An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP aranar (08/03/1440 16/11/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI