Posts

Showing posts from 2018

ƊAUƘAR CIKIN MANZON ALLAH (SAWW) DA KUMA HAIHUWARSA.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salati Matabbaci da aminci wanzajje su tabbata ga Mafi tsarkin dukkan bayi, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa. Acikin wancan darasin namu na farko, wanda muja gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp (3) munji Tarihin iyaye da kakannin Manzon Allah (saww) da yadda tsarkin nasabarsa take. Acikin wannan darasin kuma, in sha Allahu zamu ji abubuwan da suka faru tun daga daukar cikinsa har zuwa haihuwarsa (saww) da kuma abubuwan da mahaifiyarsa mai daraja ta gani na ayoyin Ubangiji da kuma girmamawa. Babban Malamin tarihin nan mai suna Ibnu Sa'ad (rah) ya ruwaito wani hadisi daga 'Yar uwar mahaifin Yazeed bn Abdillahi bn Wahab bn Zam'ah, tana cewa: "Lokacin da mahaifiyar Manzon Allah (saww) (Wato Aaminatu bintu Wahbin) ta dauki cikinsa, ta kasance tana cewa: "Ban san cewa ni ina dauke dashi ba. Kuma ban ji irin nauye-nauyen nan da Mata suke ji ba. Sai dai kawai ni ban ga al'adata ba. Kuma dama ta kas

MU SAN ANNABINMU (SAWW) - 12

Da sunan Allah Makadaici, Salati da aminci su tabbata ga Annabinmu tare da iylan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyan bayansu da kyutatawa. Wannan shine ci gaban darasinmu na Zauren Fiqhu wanda acikinsa muke kawo muhimman lamura acikin tarihin Ma'aikinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). ZAMANSA A KOGON HIRA'U ***************************** Annabi (saww) ya kasance akowacce shekara yakan kebance kansa tsawon wata guda ya tafi kogon hira'u wanda ke kan Jabalun Nur ya zauna yana tunani cikin lamarin Ubangijinsa kuma yana ibadah (bautar Allah) bisa addinin Kakansa Annabi Ibrahim (alaihis salam). Wannan tun kafin ya cika shekaru arba'in aduniya kenan. Amma bayan ya cika 'dan shekara arba'in aduniya watarana yana zaune acikin kogon sai ya hangi siffar wata Halitta mai girman gaske ta cika dukkan sasanni. Ashe Shugaban Mala'iku ne wato Jibreelu (amincin Allah ya tabbata gareshi). Yazo ya rungumeshi zuwa jikinsa runguma mai tsanani sannan y

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA

Da Sunan Allah Buwayi gagara-misali, Mai kula da lamarin bayinsa. Wanda gyangyadi bai ta'ba daukarsa ba, ballantana barci. Babu abinda ke buya gareshi daga ayyukan bayinsa acikin sarari ko duhun dare. Salati da aminci su tabbata ga Annabin da Allah ya aikoshi zuwa ga dukkan halittu amatsayin rahama garesu tare da gargadi da bushara, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mutanen kirki. Wannan ita ce fitowa ta goma sha bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu wanda ke bayani dalla-dalla game da wasu al'amuran tashin alqiyamah wacce lamarinta ke kwankwasar zukata. Babban abinda ya kamata mao karatu yayi, shine ya rika kwatanta faruwar abun a zuciyarsa domin hakika ranar nan tana tafe, kuma zata afku ne babu zato balle tsammani. Hakika idan alqiyamah ta tsaya, awannan ranar akwai masifar zafi da Qunar rana saboda kusanto da ita da za'a yi. Mutane da Aljanu gaba dayansu zasu rika zubda gumi (wato zufa) wanda sai damshinsa ya kai zurfin zira'i saba'in a Qa

ZUWA GA 'YAN UWA MATA

Aure shine mafi girman al'amari arayuwar 'Ya mace. Ta hanyarsa ne zata samu damar yin cikakkiyar bauta ga Ubangijinta, sannan ta samu damar kafa nata iyalin. Idan aure yayi jinkiri agareki, kar kiyi amfani da wannan damar wajen biyan bukatar sha'awarki ta hanyoyin da Ubangijinki ya haramta.. A'a kiyi hakuri ki kama kanki. Ki dage wajen ibadah da neman yardar Ubangijinki. Ki kyautata zato ga Ubangijinki. Shi mabuwayi ne mai hikima. Kuma duk abinda ya Qaddara miki, to kiyi fatan Allah yasa hakan ne mafi alkhairi sannan ki nemi mafita awajensa, ba wajen bokaye da 'yan bori da 'Yan duba ba.. Zina da Ma'digo da kallon hotunan batsa, da yin chatting na batsa duk Kofofin samun tsinuwa ne da kuma fushin Ubangijinki.. Ki kyautata ma kanki kiji tsoron Ubangijin da ya halicceki kar ki kai kanki ga Hallaka. Ki kiyayi hulda da mayaudaran samari wadanda ke kanki kin san ba aure ne yake kawosu wajenki ba. Mafiya yawansu zasu bata miki lokaci ne kawai. Idan kuma lokac

WASIYYAR LUQMAN ALHAKEEM (01)

Luqman (Allah shi Qara masa yarda) wani Salihin bawa ne baqar fata wanda Allah yayi masa arzikin harshe mai fasaha da hikimomi tare da samun hanyoyin warware mishkilolin al'ummah. Koda acikin Alqur'ani akwai surah guda wacce Allah ya kawo labarin Luqman da irin hikimominsa, har ma ana kiran surar da "SURATU LUQMAN". To yanzu in sha Allah zamu kawo wasu daga cikin irin hikimominsa kamar yadda suka zo a litattafan manyan Maluman Musulunci domin mu amfana da alkhairin dake cikinsu. Watarana Luqman yace ma 'dansa "Ya Kai 'dana! Kada ka aiki Jahili anatsayin 'dan aikenka. Idan har baka samu mai hikima wanda zaka aika ba, to gara ka zamanto 'dan aiken kanka. Ya kai 'Dana! ka nisanci yin Qarya. Domin hakika ita Qarya tana da zaqi abakin mutane kamar yadda naman tsuntsu yake, amma sai dai Ma'abocinta bai cika samun tsira daga gubarta ba. Ya kai 'dana! Ka rika ziyartar wajen Janazah, amma kada ka yawaita ziyartar wajen bukunkuna. Domin kuw

MU SAN ANNABINMU (05)

RASUWAR MAHAIFIYARSA MAI GIRMA (SAWW) : Bayan Mala'ikun nan sun kwantar dashi sun tsaga kirjinsa, sai Halimatus Sa'adiyyah ta dawo dashi wajen mahaifiyarsa saboda jin tsoron da takeyi bisa lafiyarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Bayan dawowarsa wajen Mahaifiyarsa da shekaru biyu wato lokacin yana da shekara shida kenan aduniya, sai tayi nufin ta ziyarci garin Yathrib (Madeenah) wajen kawunnanta Banun Najjar, da kuma Qabarin mijinta Abdullahi. Ta tafi tare da Manzon Allah (saww) tayi wadannan ziyarori, amma akan hanyarta ta dawowa sai jinyar ajali ta kamata, kuma ta rasu adaidai wani waje da ake kira "ABWA'U" kuma anan aka binneta, Qabarinta yana nan har yanzun nan. Shikenan Manzon Allah (saww) ya zamanto cikakken maraya ta bangaren mahaifansa baki daya. To alokacin nan akwai baiwar mahaifinsa wacce ake kiranta "Ummu Aymana - Barakatul Habashiyyah" ita ta kamo hannunsa suka dawo garin Makkah,  kuma shekarunsa shida awannan lokacin. ALLAHU

MU SAN ANNABINMU (06)

KOMAWARSA HANNUN KAKANSA MAI DARAJA (SAWW)  : Daga nan sai ya koma hannun Kakansa wato mahaifin mahaifinsa, mai suna Abdul Muttalibi 'dan Hashim. Ya kasance mai nuna so da Qauna ga wannan jikan nasa mai daraja (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Ya kasance duk inda zai je tare suke tafiya, ba ya yin barci sai tare dashi, hakanan wajen cin abinci ma. Kuma yasoshi fiye da sauran jikanunsa da 'ya'yansa. Ya kasance yana girmama Annabi (saww) kuma yana gaya ma mutane cewa "Akwai wani babban lamari da zai faru ga jikan nan nawa". Sai dai zamansu bai tsawaita ba, domin bayan shekaru biyu kachal sai shima ya rasu,  Kuma yabar wasiyyah ga 'daya daga cikin 'ya'yansa mai suna "Abu Talib" cewa shi zai ci gaba da kulawa da wannan jikan nasa, Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Salati da amincin Allah si tabbata bisa Annabin Rahma Ma'abocin tausayi da karamci, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da mabiyansa

MU SAN ANNABINMU (07)

Assalamu alaikum. Wannan shine darasi na bakwai acikin tarihin Shugaban Halitta (saww) kamar yadda muka gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp. ZAMANSA AWAJEN BAFFANSA : Kamar yadda muka fa'da tun da farko, bayan rasuwar Kakansa sai Annabi Muhammadu (saww) ya koma hannun baffansa mai suna Abu Talib wato dan uwan mahaifinsa wanda suka fito ciki daya. Alokacin nan yana da shekaru takwas (8) kenan aduniya. Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya taso ahannun Abu Talib cikin soyayya da mutuntawa da girmamawa, har zuwa lokacin da yayi masa aurensa na fari. Ya zauna awajensa tare da sauran yaran gidan kuma shi yayi fiche wajen kyawun halaye da dabi'u. Ba ya yin wasa ko hayaniya irin wacce sauran yara sukeyi. Haka kuma wajen cin abinci ba ya ha'dama irin wacce yara keyi. Yana cin abinda ke gabansa ne ka'dai, kuma da zarar yaci ka'dan ya isheshi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). SANA'O'INSA (SAWW)  : Ya fara sana'a ne tun yana da shekaru takwas

SHIN KA TA'BA ZUBDA HAWAYE DOMINSA KUWA?

An zageshi, an Jefeshi da duwatsu, Anyi masa jina-Jina Sahabbansa sun nemi yayi addu'a a hallakar da duniyar amma yace A'a. Maimakon haka ma sai addu'ar alkhairi yayi ma mutanensa. A lokacin da yaje ganawa da Ubangijinsa bai manta dani, da kai, da dukkan al'ummarsa ba. Sai da ya roka mana alkhairai masu yawa awajen Allah. Yayi Hijira daga Makkah zuwa Madeena. Sun biyoshi domin su kasheshi amma duk da haka bai yi musu mummunar addu'a ba.. Ya jure yunwa da Kishirwa da Zafi da sanyi duk domin al'ummarsa su samu shiriya. Aranar yakin Uhudu kafirai sunji masa rauni, amma duk da haka bai yi mummunar addu'a akansu ba. Saboda tausayi da Jin Qai irin nasa. Mutanen garin Ta'if sunyi masa wauta wacce ba'a ta'ba yin kamarta ba. Amma duk da haka bai Tsine musu ba, kuma bai yi mummunar addu'a akansu ba. Hakanan alokacin da zai bar duniya, Sai da ya tambayi Mala'ika Jibreelu ya gaya masa Alkawarurrukan da Ubangiji yayi ma al'ummarsa sannan ya

MU SAN ANNABINMU (08)

Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da ya zamanto matattarar lamarin halittu, Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah da Sahabbansa da dukkan mabiyansa har zuwa ranar tashin halittu. HADUWARSU DA BUHAIRA : Yayin da Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya cika shekaru goma sha biyu aduniya, sai baffansa Abu Talib ya fara tafiye-tafiyen kasuwanci tare dashi. Kuma daga cikin safarorin da yayi dashi, akwai tafiyar da sukayi zuwa Birnin Sham (wato Syria). Yayin da suka iso wani gari mai suna Busra wanda ke kan hanyar Sham din, sai suka sauka domin hutawa awani waje, kuma anan ne wani Malamin addinin Nasaara (Kirista) mai suna Buhaira yaga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Buhaira ya kasance yana yin ibadah ne tsawon shekaru acikin wajen bautarsa, anan ne ya hangi Manzon Allah (saww) kuma ya shaidashi ya gane cewa lallai shine Annabin Qarshe, ta dalilin wasu alamomi da ya gani. Misali ya lura da cewa Giza-gizai suna lullube wannan

MU SAN ANNABINMU (09)

Da Sunan Allah Mai rahama mai jin kai. Salati da amincinsa su tabbata bisa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da dukkan Magoya bayansa. Wannan shine darasu na 9 acikin tarihin Shugaba (saww) wanda ke zuwa muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp. HARBUL FUJJAR ****************** Bayan Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya cika shekaru ashirin (20) aduniya, wani Yaqi ya barke atsakanin Larabawa. Wato Quraishawa da Banu Kinanah ne suka ha'du suka yaqi wata Qabila mai suna "Qaisu 'Eelan". Annabi (saww) ya halarci wajen wannan yaqin alhali yana matashi, yaje tare da baffaninsa 'ya'ysn Abdul Muttalib yana kawo musu kibiyoyin harbi. Amma dai daga karshe yaqin ya Qare da sulhu atsakanin Qabilun. An kira wannan yaqin da sunan "Harbul Fujjar" ne saboda an yishi ne acikin watanni masu alfarma, wadanda ba'a saba yin yaqi acikinsu ba. HILFUL FUDHUL Bayan kammala Yaqin nan na Harbul Fujjar sai Quraishawa suka ha'

FA'IDODIN DAKE CIKIN YIN AURE :

Fa'idodin da suke cikin aure ba zasu Kididdigu ba. Amma ga wasu ka'dan daga ciki zamu lissafo kamar haka: 1. Yin aure biyayya ne ga umurnin Allah da Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). 2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (saww) farin ciki aranar lahira. Yace : "Kuyi aure ku hayayyafa. Domin ni zanyi ma sauran al'ummomi alfahari daku aranar Alkiyamah". 3. Ta dalilin aure zaka samu wanda Zai fito ta jikinka, har ya girma yana Kalmar Shahada!! "LA ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI. 4. Ta dalilin aure ne zaka samu Zuriyar da zasu yi maka addu'a bayan rasuwarka.  Wannan yana daga cikin ayyukan da  ladansu ba zai yanke ba har abada. 5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun mutum daga kalle kallen Haramun, sannan ya kare masa al'aurarsa daga Zina. 6. Ta dalilin aure ne zaka samu damar taimaka ma 'Yar uwarka Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta kenan daga Zina. 7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar addininka, da ninkawar lad

MU SAN ANNABINMU (SAWW) - 1

NASABARSA : ************** Shine Shugabanmu Muhammadu 'dan Abdullahi 'dan Abdul Muttalibi 'dan Hashim 'dan Abdu Manafi 'dan Qusayyu 'dan Kilabu 'dan Murratu 'dan Ka'abu 'dan Lu'ayyu 'dan Ghalibu 'dan Fihru 'dan Maliku 'dan Nadhru 'dan Kinanatu 'dan Khuzaimah 'dan Mudrikah 'dan Ilyas 'dan Mudhar 'dan Nizaar 'dan Ma'addu 'dan 'Adnan shi kuma Adnan yana daga cikin jikokin Annabi Isma'il (as) shi kuma 'dan Annabi Ibraheem (as). Nasabah ce tsarkakakkiya wacce babu wani datti ko Qazanta irin ta zamanin jahiliyyah da ta ta'ba ratsata. Kowanne daga cikin iyayensa da kakanninsa tsarkakakke ne kuma mafi nagartar mutanen zamaninsa. Haka kuma iyayensa mata dukkaninsu tsarkaka ne madaukaka acikin jama'ar zamunnansu. Shi da kansa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace " NI ZA'BABBE NE DAGA CIKIN ZABABBU DAGA CIKIN ZABABBU ". Allah ya zabi zuriyar gidan

MAGANIN NAKUDA DA YAWANCIN CUTUKAN MATA

Daga cikin mafiya girman fa'idodi game da maganin nakuda, asamu: 1. HABBATUS SAUDA COKALI 1. 2. ALBABUNAJ COKALI 1. Adafasu da ruwa kofi guda. idan sun tafasa asauke atace asanya zuma gwargwadon yadda ake so sannan asha da duminsa. Idan mace tana shan wannan zata samu saukin laulayin ciki. kuma idan tazo haihuwa ma abin zaizo da sauki Bi-iznillahi. Hakanan Idan aka samu Man Habbatus Sauda Mai kyau (Made in Saudi, ko Pakistan, ko Sudan ko egypt) tare da Man Albabunaj (Chamomile Oil) ahadasu arika sanya cokali guda acikin Shayi (Tea) ko Ruwan dumi, Idan mace tana sha zata samu sauki daga yawancin cututtukan da mata suke fama dashi kamar: * Kaikayin gaba * Fitar farin ruwa. * Rikicin jinin al'ada. * Matsanancin Ciwon Mara. * Namijin dare. * Ciwon ciki. * Qarancin barci. * Daukewar sha'awa. * Rashin ruwan nono. Idan matayen aure da 'Yan mata suka riki irin wadannan magungunan na Islama sun ishesu ba sai sunje suna jele a asibiti ba. Domin zuwan mace ta bude

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH 112)

HALARTAR JANA'IZA ********************** Hadisi daga Khalid bn Ma'adan daga Sayyiduna Abu Umamah (radhiyallahu anhu) cewa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace : "DUK WANDA YA SALLACI SALLAR JUMA'AH, KUMA YA AZUMCI WUNINTA, KUMA YA DUBA MARAR LAFIYA, KUMA YA HALARCI JANAZAH, KUMA YA HALARCI DAURIN AURE, ALJANNAH TA WAJABTA GARESHI". ADUBA MU'UJAMUL AUSAT (Juzu'i na 3 shafi na 23). Allah yasa mu dace da samun rahamarsa da falalarsa da rangwamensa ameen. Hakika dukkan wadannan abubuwan da aka lissafa, mafiya yawansu ayyuka ne dake Qara dankon zumunci da Qaunar juna atsakanin al'ummah. Kuma yinsu yana sanya farin ciki a zuciyar mumini kuma yana janyo samun yardar Allah Mai rahama. Ya Allah ka datar damu duniya da lahira. Ka bamu yardarka don falalarka da rahamarka da soyayyar da kake yiwa bayinka. Salati da aminci da albarka da martabobi su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da Saliha

JARUMTAKAR SAHABBAI (02)

LABARIN WANI UBA DA 'DANSA (RA) Aranar da za'a fita zuwa yaqin badar, lokacin da Annabi (saww) ya sanar da Sahabbai cewa duk wanda yake da iko ya fito a tafi, wani baqon al'amari mai ban mamaki ya faru tsakanin Wani Sahabi mai suna Sa'adu bn Khaythamah da mahaifinsa Khaythamah bn Harith (Allah ya yarda dasu). Yayin da sanarwar fita yaqin tazo kunnensu sai Khaithamah din ya kira 'dansa yace masa "Ya kai 'dana! Hakika ayau din nan sai 'dayan cikinmu ya fita, 'daya kuma ya zauna a gida ya kula da Mata da Qananan yara. Don haka ni zan fita (zuwa badar din) kai kuma ka zauna agida ka kula da Mata da Qananan yara". Sai Sa'adu yace "Ya Babana! Wallahi wannan ba zai yiwu ba. Domin ni nafi ka kwadayin fita yaqin, Kai kuma kafi ni bukatuwa zuwa ga zaman gida. Don haka ni zan fita kai kuma ka zauna agida". Sai Baban yace "Ya kai Sa'adu sa'ba mun zakayi?  Wato ba zaka bi umurnina ba!!". Sai Sa'adu yace "Hakika

MAI TACECCEN FARI (SAWW)

Ya Allah kayi salati bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu Mai taceccen farin fatar jiki, ma'abocin yalwatattun idanuwa masu kyawu da kwarjini da hasken fuska,   Mai mutukar farin cikin idanu da baqin kwayar cikinsa tare da ratsina ja wanda ke nuna alamar Qarfin jiki da zuciya tare da jarumtakarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Kayi salati da tasleemi gareshi Ma'abocin yalwataccen gashin kai, gashin nasa baqi ne mai sheqi kuma yayi liflif akan kafadunsa. Mai yalwataccen goshi tare sissiran karan hanci, da mayalwacin gashin gira masu kyawu da kwarjini. Mai fararen hakora jerarru,  ga wushirya mai fidda haske da Qamshi yayin da yake magana. Kwarjini ya lullube murmushinsa, ga tawadhu'unsa ya mamaye dukkan lamarinsa (saww). Kayi salati da tasleemi gareshi Ma'abocin Manyan damatsu mai zara-zaran yatsu,  mai yalwar tafin hannu bisa ma'ana da zahiri. Mai Madaidaicin ciki ne shi tare da yalwar Qirji. Cikinsa da Qirjinsa sun daidaita da juna, kuma akwai wani jerarr

KU DUBI IRIN WANNAN SOYAYYA!!

Bayan an dawo daga Yakin Uhudu, kasancewar shine Yaqi na farko wanda Musulmai da yawa sukayi shahadah, Sai garin Madeena ya cika da kururuwar Mata da Qananan yara. Yayin da Manzon Allah (saww) yaji wasu mata daga dangin Banu Abdil-Ash'hal suna ta rusa kuka saboda mamatansu, Sai hankalinsa ya tashi. Ya tuna da Baffansa wato Sayyiduna Hamzah bn Abdil Muttalib (rta). Sai yace: "SAI DAI KUMA SHI HAMZA BASHI DA MASU YI MASA KUKA". Daga jin wannan Qaulin sai gaba daya Matayen mutanen Madeenah suka taho suka zauna suka fara rusa kuka domjn su taya Manzon Allah (saww) bakin cikin rabuwa da Baffansa. Suna ta kuka cikin dare har Manzon Allah (saww) yayi barci. Yayin da ya farka yaji har yanzu suna tayi, sai yace: "Ya Kaitonsu, har yanzu suna zaune anan? Ku umurcesu su koma (gidajensu) Kuma bayan wannan ranar kar su sake yin kuka bisa wani Mamaci". ADUBA : - ÃLUL BAITI HAULAR RASOOL (shafi na 101). - SUNANU IBNI MAAJAH (hadisi na 1591). Zauren Fiqhu, wannan yana n

MADUBIN DUBAWA (64)

Sa'eed bn Sulaiman yace "Na kasance acikin garin Makkah tare da Abdullahi bn AbdilAzeez  Al Umariy ('Daya daga cikin Maluman Tabi'ai masu gudun duniya). Alokacin nan Khalifah Harunar Rasheed yazo wajen aikin hajji. Sai wani mutum yace wa Abdullahi Al Umariy, "Ya kai baban Abdurrahman! Gashi chan Sarkin Muminai (Harunar Rasheed) yana Sa'ayi (wato tafiya tsakanin Safa da Marwah) kuma duk an bar masa wajen sa'ayin!". Sai shi Abdullahi Al Umariy din yace ma mutumin "Kada Allah ya saka maka da alkhairi domin ka dora min wani aiki wanda na wadatu da barinsa". Sai ya tashi ya dauki takalmansa ni kuwa ina binsa abaya. Sai ga Harunar Rasheed ya taho daga Marwah ya nufi Safaah.. Sai Abdullahi Al Umariy yayi kiransa yace "YA KAI HAROON!". Da khalifan ya waiwayo ya ganshi sai yace "Amsawarka Ya baffana!". Sai yace "Mu hau dutsen Safaa". Yayin da suka hau sai yace ma Khalifan "Sanya idanuwanka wajen 'Dakin All

FA'IDODIN YIN SADAQAH (DAGA ZAUREN FIQHU)

Ya kai 'Dan uwa Musulmi!! Ya ke 'Yar uwa Musulma!! Shin ko kun san cewa sadaqah tana da Mutukar amfani arayuwar 'Dan Adam? Bari kuji wasu daga cikin fa'idodin dake cikinta : 1. Sadaqah wata Qofa ce daga kofofin samun shiga Aljannah. 2. Acikin dukkan ayyukan lada, Sadaqah tana daga sahun gaba. Kuma mafificiyar sadaqah ita ce "Ciyar da abinci domin Allah". 3. Sadaqah tana inuwantar da Ma'abotanta aranar Alqiyamah, Kuma tana 'Yantar dashi daga shiga Wuta. (Gwargwadon yawan sadaqarka, shine gwargwadon ni'imar da zaka shiga aranar Alqiyamah). 4. Sadaqah tana bushe fushin Ubangiji. (Allah yana son masu yinta, don haka ba zai yi fushi da kai ba). 5. Sadaqah tana kiyaye mutum daga Azabar Qabari. 6. Sadaqah ita ce mafificiyar kyautar da zakayi ma Mamacinka. 7. Sadaqah, Ubangiji ne ke rainonta har sai ranar Alqiyamah za'a nuna maka ladanta. 8. Sadaqah tana tsarkake zuciya daga Qazantar nan ta rowa da kyashi. 9. Sadaqah tana janyo maka soyayyar

RANAR HAIHUWARSA (SAWW)

Ko kasan cewa yayin da Nana Ãminatu bintu Wahbin ta dauki cikin Manzon Allah (saww) ta kasance akowanne dare na watannin goyon cikin tana ganin Annabawa da Manzanni (alaihimus salam) suna zuwa gareta suna gaisuwa tare da yi mata albishirin cewa zata haifi Shugabansu baki daya (saww). Ko kasan cewa alokacin da aka haifi Manzon Rahama (saww) akwai wani gagarumin hasken da ya fito tare dashi, tun daga garin Makkah har sai da ya haskaka manyan Katangun garuruwan Qasar Sham.. Ko kasan cewa Shi komai nasa daban yake, ranar haihuwarsa anji muryoyi daban daban suna yin murna da zuwansa. A daren saukarsa duniya, an wayi gari dukkan kujerun sarakunan duniya sun kife, Hakanan dukkan gumaka da kayan tsafi sun wayi gari kife akan fuskokinsu. Ya kasance shine mafi kyawun mutane, kuma mafi daidaiton halitta. Jikinsa yana haske, fatarsa tana Qamshi, hakoransa suna haske. Bashi da inuwa, Qura bata sauka ajikinsa, Quda ba ya hawa kan fatarsa, Kuma idan yana tafiya akan rairayi ba'a ganin alamar

YADDA AKE KARYA SIHIRI DA IZININ ALLAH.

Idan kana tunanin anyi maka sihiri ko anyi ma wani 'Dan uwanka, Ko kuma matsalar Maita (Kambun Ido) to ga hanya mai sauki kuma halastacciya wacce Zauren Fiqhu ya dauko daga cikin irin fatawoyin da muke amsawa akan shafukanmu na Internet. Da farko dai dole ka sanya hakuri da Tawakkali da tsoron Allah acikin zuciyarka. Ka fidda Qiyayya ko zargi atsakaninka da duk wani Musulmi. Sannan ka aikata wannan fa'idar : 1. Asamu ruwa cikin Bokiti, ka samo ganyen Magarya guda 7 ka dandakasu akan dutse da dutse sannan ka zuba acikin ruwan. Ka tsoma babban yatsan hannunka na dama acikin ruwan. Ka kusanto da bakinka daf da ruwan. Sannan ka karanta wadannan ayoyi da surorin : 1.  Fatiha. 2. Suratul Baqarah ayah ta 1-5. da kuma ayah ta 102-103. da kuma ayah ta 163-164. Da kuma ayah ta 255 - 257. Da kuma 285-286. 3. SURATU AALI 'IMRAAN : Ayah ta 18-19. 4. SURATUL A'ARAF : 54-56. da kuma 117-122. 5. SURATU YUNUS (AS) : Ayah ta 81-82. 6. SURATU TAAHA (AS) : Ayah ta 69. 7. SURATUL

MATSAYIN SAYYIDUNA ABUBAKAR (RADHIYALLAHU ANHU) AWAJEN AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM).

Hakika alaqar dake tsakanin Ahlul Baiti da manyan Sahabban Manzon Allah (saww) alaqah ce dake kunshe da mutukar Qauna da girmamawa tare da kulawa da hakkokin juna. Sahabbai suna girmama Ahlul baiti saboda kusancinsu da Manzon Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) su kuma Ahlul Baiti suna girmama Sahabbai saboda yardar da suka samu awajen Allah da Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) da taimakon da sukayi wa addininsa. Muhammad Ibnul Hanafiyya, daya daga cikin 'ya'yan Sayyiduna Aliyyu (rta) kuma Kogin ilimi, babban Malami acikin Tabi'ai, yace "Na Tambayi Mahaifinmu "Shin wanene mafi alkhairin mutane, bayan Manzon Allah (saww)? Sai yace min "Abubakar" Nace sannan sai wa? sai yace "Umar." Ina jin tsoron kar yace sai Uthman. sai nace masa sannan sai kai? Sai yace min "A'a.. ni dai daya ne daga cikin al'ummar Musulmi". (Bukhary juzu'i na 7, shafi na 24. hadisi mai lamba 2,671). Duk da cewa ya faɗi

LABARI MAI BAN-TSORO

Qissah ce daga Shaikh Abdullahi bn Ahmad Al-Mu'azzin (rah) yace : "Na kasance ina yin 'Dawafi a dakin Ka'abah sai naga wani Mutum (Dattijo) ya Qanqame rigar Ka'abah yana Tsula kuka yana addu'a yana cewa : "YA ALLAH KA FITAR DANI DAGA DUNIYAR NAN INA MUSULMI". Yana fa'da yana Maimaitawa kuma ba ya Qara komai akan haka. Sai nace masa "Ya Kai Bawan Allah! Shin ba zaka Qara komai akan wannan ba?". Sai ya juyo gareni yace "Da ache kasan labarina da ba zaka ce haka ba". Sai nace "Menene labarin naka?". Sai yace "Na Kasance ina da 'Yan uwa Maza guda biyu. Babban cikinsu ya kasance shi Ladani ne (Mai Kiran Sallah). Yayi shekaru Arba'in (40) yana kiran sallah don neman lada. Amma yayin da Mutuwa tazo gareshi sai ya bukaci mu kawo masa Mus'hafi (Wato Alqur'ani cikakke). Har muna Tsammanin cewa watakil zai yi Tawassuli dashi ne domin neman albarka. Amma yayin da ya karbi Alqur'anin ya rikeshi da hann

FALALAR AZUMIN ASHURA (DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP)

Wannan cikakken bayani ne daga ZAUREN FIQHU dangane da Azumin Tasu'ah da Ashurah. Hakika ranar ashura, rana ce wacce babu irinta acikin ranakun shekara baki daya. Domin kuwa rana ce wacce manyan Muhimman al'amura na tarihi suka faru acikinta. Rana ce wacce addinin Musulunci ya sunnanta yin azuminta domin koyi da Manzon Allah (saww). Kamar yadda zamu gani acikin hadisai Sahihai masu zuwa in sha Allahu. Daga Abu Hurairah (ra) yace "An tambayi Manzon Allah (saww) "Shin wacce Sallah ce tafi falala bayan Sallolin farillah?". Sai yace ".YIN SALLAH CIKIN TSAKAR DARE". Sai aka ce "Wanne Azumi ne yafi falala bayan na Ramadhan?" Sai yace: "WATAN NAN NA ALLAH WANDA KUKE KIRANSA ALMUHARRAM". (Muslim da Ahmad da Abu Dawud ne suka ruwaitoshi). Kunga wannan hadisin ya nuna mana cewa falalar wannan azumin da akeyi acikin Almuharram wato Ashura da Tasu'ah kenan sun zarce falalar yin azumi awani watan  in banda Ramadhan. Daga Sayyiduna Mu&#

MATSALAR CIN HANCI A NIGERIA

Shekaru biyu da suka wuce naje Qasar Togo sannan na wuce Kamaru (Cameroun) kuma na shiga airport na kowacce Qasa. Amma har naje na dawo babu inda aka tambayeni "NA-GORO" sai anan Nigeria. Kuma abun kunya ma a international airport dinmu na Lagos nan ne abun yafi Qamari. Ba sani ba sabo, idan kazo babu "Yellow card" sai ka sayeshi akan Naira dubu uku ko hudu (abun naira 300) in ba haka ba, ba zaka wuce ba. Haka ma Ma'aikatan dake duba passport din matafiya, sai sun tambayeka "NA GORO" kafin ka wuce ta gaban teburinsu. Duk wanda ya shigo Nigeria daga Nijar ta kan bodar Illela ko Kongolam zai baka labarin irin cin zarafin da ma'aikatan Nigeria suke yiwa 'Yan Qasar Nijar (Abun tausayi wallahi). Ga Misali : Duk lokacin da zasu shigo Qasar nan sai Ma'aikatan sun leka cikin motocin sun kirge adadinsu. Kuma kowannensu sai ya bayar da ₦200 in ba haka ba, sai dai ya koma Qasarsa.   Sannan idan sunzo Kano sunyi sayayyar kaya, akan hanyar komawars

MUMMUNAN ZATO

Mummunan zato yana daga cikin manyan kaba'irori da Allah ya haramta. Idan mutum ya zamanto mai yawan yiwa jama'a mummunan zato, da sannu sai ya mayar da masoyansa sun zamto makiyansa.. Da sannu zai zamanto Azzalumi kuma magulmaci.. Zai zalunci musulmai wajen yi musu yarfe da Qage da Qazafi. Kuma duk suna daga cikin manyan zunubai.. Watarana zai iya yin zancensu awajen wasu, yace wane yayi mun kaza da kaza, wane bai kyauta mun ba.. Alhali kuma ba lallai ne hakan ya zamto gaskiya ba. Daga cikin hakkokin da kowanne Musulmi yake dashi akan 'yan uwansa Musulmai, akwai cewa "KADA AYI MASA ZATO SAI NA ALKHAIRI" Sai dai idan ya aikata abinda ya keta alfarmar shari'a, to anan kuma Jama'ar musulmai suna da damar yin Qararsa, kuma shari'a tana da damar yin bincike kafin yanke hukunci akansa. Kyautata zato ga 'yan uwa da makusanta da masoya, yakan kawo hutun zuciya da sulhu da hadin kai atsakanin juna. Bayan kuma dimbin ladan dake cikin yin haka. Amma shi

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (107)

SALATI GA SHUGABA ( SAWW ) ****************************** Manzon Allah (saww) yace "Duk wanda yayi salati bisa Annabi Muhammadu kuma yace "Ya Allah ka saukar dashi awajen zama mafi kusanci gareka aranar Alkiyamah" to samun cetona ta wajabta gareshi. Imamul Bazzar ya ruwaito hadisin acikin Musnadinsa, da Tabaraniy acikin Mu'ujamul Awsat da Mu'ujamul Kabeer, Kuma sun ce isnadin hadisin yana da kyau. GA YADDA MALAMAI SUKA FITAR DA SIFFAR SALATIN : اللهم صل على محمد وعلى آله وأنزله المقعد المقرب عندك يوم القيامة Allahumma Swalli 'ala Muhammadin wa 'ala aalihi wa anzilhu Al Maq'adal muqarraba 'indaka yaumal qiyamah. Aduba shafi na 3 acikin littafi mai suna AL ISHRAQATUS SANIYYAH, sharhin Shama'ilul Muhammadiyyah na Imamut Tirmidhiy wanda Shaykh Hisham Alkamil ya rubuta. DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (01/01/1440  09/NOV/2018).

MAI DADIN SUNAYE (SALLAL LAHU ALAIHI WA ALIHI WA SALLAM (10)

Da Sunan Allah Makadaicin da bashi abokin tarayya.. Salati da aminci mafiya cika da martaba su tabbata bisa Cikakken Bawan Allah, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu alfarma, tare da dukkan Magabata na kwarai da waliyyan Allah da dukkan nagartattun bayinsa. Wannan shine karo na goma (10) acikin darasin Zauren Fiqhu wanda acikinsa muke yin sharhi tare da bayanai takaitattu game da ma'anonin wasu daga sunayen Shugaban mutanen farko da karshe (Sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). 17. SAYYIDUN : WATO SHUGABA (SAWW). Shine Shugaban halittun farko da Karshe. Tun daga kan Banu Adam har Mala'iku da Aljanu da dabbobi da dukkan abinda ke karkashin wannan Ma'anar. Acikin hadisin da Imamul Bukhariy ya ruwaito, Manzon Allah (saww) yace "NINE SHUGABAN 'YA'YAN ADAM ARANAR ALQIYAMAH, KUMA BA ALFAHARI NAKEYI BA". Kuma yace "NINE MAFI GIRMA AWAJEN UBANGIJINA ARANAR ALQIYAMAH". (Riwayar Tabaraniy). Kuma yace "ADAMU

FA‹IDODIN SALATIN ANNABI (SAWW) DAGA ZAUREN FIQHU (KASHI NA FARKO

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabin da Allah ya aikoshi domin rahama ga dukkan Talikai, tare da iyalan gidansa da dukkan Sahabbai da bayin Allah Salihai. Salatin Annabi (saww) wata irin ibadah ce wacce babu irinta acikin dukkan ibadun da Mumini zai iya yi da harshensa. Tana kunshe da falala wacce 'Dan Adam ba zai san iyakarta ba. Domin ita wata babbar hanya ce wacce take nuna jin Ƙai irin na Allah ga bayinsa. Malamai da yawa sunyi rubuce rubuce akan sha'anin Salatin Annabi (saww) Musamman bangaren falalarta da kaifiyyoyinta. Acikin littafinsa mai suna "KHULASATUL ADILLATISH SHAR'IYYAH FIR RADDI 'ALA TASA'ULATIL HASHAWIYYAH, Babban Malamin nan Muhammad Miftah bn Salih ya kawo fa'idodin Salatin Annabi (saww) har guda Sittin da biyar (65). Amma guda arba'in ya cirosu ne daga littafin Ibnul Qayyim Al-Jawziyyah mai suna JILA'UL AFHAAM FIS SALATI WAS SALAM 'ALA KHAIRIL ANAAM, shafi na 129-135. Ga fa'id

HANYOYIN DA MUTUM ZAI BI DOMIN YIWA KANSA GARKUWA DAGA SHARRIN SHAITANUN ALJANU

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ************************************ _*Salati da aminci su tabbata ga Shugaban Annabawa da Manzanni tare da iyalan gidansa da Sahabbansa.*_ _Malaman Musulunci sun fadi wasu abubuwa guda goma masu sauki, wadanda duk wanda ya lazimcesu Allah zai kiyayeshi daga sharrin Shaitanun Aljanu. Ba zasu iya shiga jikinsa ba.. Da izinin Allah._ *1. ISTI'AZAH (NEMAN TSARIN ALLAH DAGA SHARRINSU) :* _Allah (swt)  yana cewa:_ _*"IDAN KUMA WANI ZUNGURA YAZO MAKA DAGA SHAITAN, TO KA NEMI TSARI DA ALLAH. DOMIN SHI (ALLAH) SHINE MAI JI, KUMA MASANI".*_ _Wato yayin da zaka nemi tsarin Allah daga sharrinsu, dole ne ka Qudurce cewar Allah yana tare dakai, yana jin ka, kuma ya fika sanin halin da kake ciki, kuma Shi yake da ikon kareka da kiyayeka daga sharrinsu._ *2. KARANTA AL-MU'AWWIZATAINI (WATO FALAQI DA NAASI) :* _suna da Muhimmanci sosai tunda Manzon Allah (saww)  yace_ _*"BA'A TABA YIN ADDU'AR NEMAN TSARI KAMARSU BA".*_ _Kuma shi k

MATSALAR CIN HANCI A NIGERIA

Shekaru biyu da suka wuce naje Qasar Togo sannan na wuce Kamaru (Cameroun) kuma na shiga airport na kowacce Qasa. Amma har naje na dawo babu inda aka tambayeni "NA-GORO" sai anan Nigeria. Kuma abun kunya ma a international airport dinmu na Lagos nan ne abun yafi Qamari. Ba sani ba sabo, idan kazo babu "Yellow card" sai ka sayeshi akan Naira dubu uku ko hudu (abun naira 300) in ba haka ba, ba zaka wuce ba. Haka ma Ma'aikatan dake duba passport din matafiya, sai sun tambayeka "NA GORO" kafin ka wuce ta gaban teburinsu. Duk wanda ya shigo Nigeria daga Nijar ta kan bodar Illela ko Kongolam zai baka labarin irin cin zarafin da ma'aikatan Nigeria suke yiwa 'Yan Qasar Nijar (Abun tausayi wallahi). Ga Misali : Duk lokacin da zasu shigo Qasar nan sai Ma'aikatan sun leka cikin motocin sun kirge adadinsu. Kuma kowannensu sai ya bayar da ₦200 in ba haka ba, sai dai ya koma Qasarsa.   Sannan idan sunzo Kano sunyi sayayyar kaya, akan hanyar komawars

KUNDIN SOYAYYA (01)

Kar kuji na ambaci kalmar "Soyayya" kuyi zaton ko soyayyar wani ko wata nake nufi.. A'a ni ina nufin shiga cikin kundin soyayyar Masoyin Allah ne, Zababben Allah (saww) : Zamu leka cikin Kundin kaunarsa domin mu karanto wasu kalmomin Soyayya da yabo wadanda suka fito daga bakin Magabata na kwarai : 1. NANA KHADIJAH BNT KHUWAILID (RA) TA CE: "Da ache kowanne dare da rana zan samu shimfidar Annabi Sulaimanu (as) da kuma Mulkin Sarakunan Farisa, Qimarsu awajena ba zai kai koda fiffiken sauro ba.. In dai idanuna bai kasance yana kallon fuskarka ba". "Wallahi har abada Allah ba zai Wulakantaka ba". 2. HASSANU BN THABIT (RA) : "IDANUNA BASU TA'BA KALLON WANDA YAFIKA KYAWU BA. KUMA MATA BASU TA'BA HAIFUWAR WANDA YA FIKA KYAWU BA". "YAYIN DA NAGA HASKENSA YA BULLO, SAI DA NA SANYA HANNUNA AKAN IDONA SABODA KWARJINI". 3. IMAM ALIYU BN ABI TALIB (RA)  YACE: "BAN TA'BA GANIN WANI IRINSA KAFINSA BA. KUMA ABAYANSA MA B

FA'IDODIN YIN SADAQAH DAGA ZAUREN FIQHU

Ya kai 'Dan uwa Musulmi!! Ya ke 'Yar uwa Musulma!! Shin ko kun san cewa sadaqah tana da Mutukar amfani arayuwar 'Dan Adam? Bari kuji wasu daga cikin fa'idodin dake cikinta : 1. Sadaqah wata Qofa ce daga kofofin samun shiga Aljannah. 2. Acikin dukkan ayyukan lada, Sadaqah tana daga sahun gaba. Kuma mafificiyar sadaqah ita ce "Ciyar da abinci domin Allah". 3. Sadaqah tana inuwantar da Ma'abotanta aranar Alqiyamah, Kuma tana 'Yantar dashi daga shiga Wuta. (Gwargwadon yawan sadaqarka, shine gwargwadon ni'imar da zaka shiga aranar Alqiyamah). 4. Sadaqah tana bushe fushin Ubangiji. (Allah yana son masu yinta, don haka ba zai yi fushi da kai ba). 5. Sadaqah tana kiyaye mutum daga Azabar Qabari. 6. Sadaqah ita ce mafificiyar kyautar da zakayi ma Mamacinka. 7. Sadaqah, Ubangiji ne ke rainonta har sai ranar Alqiyamah za'a nuna maka ladanta. 8. Sadaqah tana tsarkake zuciya daga Qazantar nan ta rowa da kyashi. 9. Sadaqah tana janyo maka soyayyar

MAGANARSA DA DABBOBI (SAWW) 07

Alqadhy 'Iyadh bn Musa Alyahsubiy (Allah ya rahamsheshi) ya ruwaito acikin littafinsa Mai albarka (Ash-Shifa) aciki Qissar makiyayin dabbobin nan wanda kura tayi magana dashi, mutumin yana cikin tsananin mamaki sai kurar tace masa "Ai kai ne babban abun mamaki.. Kana tsaye akan tumakinka kuma ka bar wannan Annabin wanda Allah bai ta'ba aiko Annabin da ya fishi girma ba (baka je ka bada gaskiya dashi ba). "Kuma yana da daraja awajen Allah tunda har an bude masa Qofofin Aljannah kuma ga 'Yan Aljannar nan an bude musu suna kallon Yaqin Sahabbansa. Babu abinda ke tsakaninka dashi sai wannan Surkukin. (Kaje kayi imani dashi) Sai kaima ka zamto acikin rundunar Allah". Sai shi Makiyayin yace mata "To wa zai kula min da tumaki na?". Sai tace "Ni zan kula maka dasu har sai ka dawo". Sai ya sallamar da dabobinsa ga Kurar, kuma ya tafi yaje ya tarar da Manzon Allah (saww) awajen Yaqi, ya bashi labarin dukkan avidna ya faru tsakaninsa da kurar, ku

MAGANIN CHUTUKAN FATA :

TAMBAYA TA 2554 ******************* Assalamu Alaikum malam ya iyali? ya hakuri da jama'a?  Ubangji Allah ya saka da gidan aljanna, don Allah malam magani nikeso ataimaka mani dashi, wanda ya danganci fata, wata irin cutace nike fama da ita shidai ba makero ba amma azababben kaikayi gareshi idan ina sosashi sai yayi bororo ya fashe kamar wuta ,wani lokaci ma har jini yake idan ina sosawa nasa magunguna da dama amma haryanzu sai dai sauki, kuma da ga kafafu da hannu ne kadai amma yanxu ya bulla har ga jiki.Bissalam. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Daga cikim jerin magungunan Musulunci wadanda ake magance irin wadannan chutukan dasu akwai : - Man Jirjir, - Man kwakwa. - Man Ghelo. - Man Kadanya. - Man Alayyadi. - Man Zaitun. - Man Aloe Vera. Shin Man Zaitun ana amfani dashi akan matsalolin fata wadanda basuyi zurfi ba. Saboda shi bashi da zafi. Amma idan abu yadan yi nisa sai kiyi amfani da sauran, daya bayan daya. Ko kuma ki hadasu waje gud