Posts

Showing posts from 2016

YA SAKETA ACIKIN IDDAH

YA QARA SAKINTA ACIKIN IDDAH TA MBAYA TA 2025 ******************* Aslkm Wa rahmatullahi Wa barakatuhu. Don Allah zauren Fiqhu, Ina son a kara warware min wannan matsalan. Mijina ne ya ce nasakeki saki daya, toh ina cikin wancan iddah ban kare ba sai yace ya kara daya. Shine nake son inji sakin na biyun yayi ko baiyi ba?. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Eh lallai ya halatta ga Mijinki ya Qara yin wani sakin bayan wannan na farkon da yayi, koda kina cikin iddah. Kuma sakin ya yiwu. Da ache kin riga kin Qare iddar farko ne, to kin fita daga hannunsa baki daya. Bashi da wannan damar. Amma ayanzu kam wannan sakin ya yiwu. Idan kika kammala jininki uku shikenan kina da damar kije ki auri wani sabon Mijin. Allah ya sawwake, Allah ya daidaita tsakanin dukkan Ma'auratan da suke cikin rikici. WALLAHU A'ALAM. D AG A ZAUREN FIQHU 14-11-2016 (14-02-1438).

MAGANIN CIWON TSAKUWAR UWAR HANJI

TAMBAYA TA 2021 ******************** Assalamu alaikum Zauren Fiqhu, fatan alkhairi da godiya ga Malam. Ni dalibi ne a wannan zaure mai albarka na shafin facebook, Ina fama da wani irin ciwon ciki ne wanda idan ya rike ni ko tashi tsaye inyi tafiya mai kyau bana iyawa, kuma nayi scanning har sau uku amma ba komai take nunawa ba, sai yau danayi awani asibitin sukayi confirming appendixes ne. Don  Allah Malam ban Sani ba ko akwai wasu magungunan da zan iya amfani dasu Wanda ba sai anyimin operation ba. JAZAKUMALLAH BI AHSANUL KHAIR. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Da farko dai muna yi maka fatan alkhairi da fatan Allah ya baka lafiya daga dukkan abinda ke damunka. Akwai abubuwa da dama a likitancin Musulunci wadanda sukan magance irin wannan ciwon in sha Allahu. Kamar yadda bayanai suka gabata anan Zauren Fiqhu. Ga wasu nan kamar haka : 1. Ka samu Garin Kustul Hindi cokali 7, garin Shammar cokali 7, Garin Habbatus sauda cokali 7, garin Kirfa cokali u

MAGANIN CIWON TSAKUWAR UWAR HANJI

TAMBAYA TA 2021 ******************** Assalamu alaikum Zauren Fiqhu, fatan alkhairi da godiya ga Malam. Ni dalibi ne a wannan zaure mai albarka na shafin facebook, Ina fama da wani irin ciwon ciki ne wanda idan ya rike ni ko tashi tsaye inyi tafiya mai kyau bana iyawa, kuma nayi scanning har sau uku amma ba komai take nunawa ba, sai yau danayi awani asibitin sukayi confirming appendixes ne. Don  Allah Malam ban Sani ba ko akwai wasu magungunan da zan iya amfani dasu Wanda ba sai anyimin operation ba. JAZAKUMALLAH BI AHSANUL KHAIR. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Da farko dai muna yi maka fatan alkhairi da fatan Allah ya baka lafiya daga dukkan abinda ke damunka. Akwai abubuwa da dama a likitancin Musulunci wadanda sukan magance irin wannan ciwon in sha Allahu. Kamar yadda bayanai suka gabata anan Zauren Fiqhu. Ga wasu nan kamar haka : 1. Ka samu Garin Kustul Hindi cokali 7, garin Shammar cokali 7, Garin Habbatus sauda cokali 7, garin Kirfa cokali u

BANKUNAN AJIYAR RUWAN MANIYYI

Yanzun nan ina zaune sai naga shigowar wata wasika daga wani 'Dan uwa kuma member a Zauren Fiqhu Whatsapp -1. Yana jan hankalina zuwa ga karanta wani bayani da ya kwafo ya turo mun. (Daga shafin wata Jaridar Qasar nan). Wato bayanin yana kunshe ne da wani Quduri wanda wata Cibiyar binciken yanayin rayuwa da kuma tattalin arzikin Nigeria (NISER) dake Ibadan ta gabatar. Cibiyar tayi kira ne ga Gwamnatin Tarayyar Nigeria cewar ta kafa "SPERM BANKS" (Rumbunan ajiyar ruwan Maniyyi da Qoyayyen Halitta) a sasannin Nigeria. Cibiyar ta gabatar da wannan kiran ne acikin wata takarda wacce daya daga cikin Wakilanta DR THERESA ORIAKU EMORDI ta Jami'ar Obafemi Awolowa ta gabatar awajen wata Seminar. Sun bukaci ma asanya Qudurin ya zama doka a Qasar nan cewa Matsalar rashin haihuwa dole sai an magance matsalar rashin haihuwa atsakanin Ma'aurata. Shi dai wannan bankin ajiyar Maniyyi idan har an Qirkireshi, to zai bada damar kowanne mutum zai iya zuwa

HUKUNCIN AMSA SALLAMAR WANDA BA MUSULMI BA

TAMBAYA TA 2001 ******************** Assalamu alaikum. Allah ya qarawa malam Eamani ya jiqan iyaye. Ameen, tambaya nake roqon a amsa min. Yaya hukuncin Wanda ya shaaku da Wanda ba musulmi ba kuma ya dauke shi a matsayin aboki? kuma shin ya kamata a mayar ma Wanda ba musulmi sallama  idan yace ma Assalamu alaikum?. Dafatan malam zai samu damar amsa tambayata. daga dalibinka Ibraheem I g AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Allah Madaukakin Sarki ya umurcemu da cewa kada mu riki Yahudu da Nasaara amatsayin Masoya ko Majibinta garemu. Ba don komai ba, sai domin sharrin da irin hakan zai haifar ga rayuwarmu da addininmu. Allah Madaukakin Sarki yace : "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI! KADA KU RIKI YAHUDU DA NASAARA AMATSAYIN MAJIBINTA (WATO ABOKAI KO MASOYA) SASHENSU MAJIBINTA NE GA SASHE. DUK WANDA YA JIBINCESU DAGA CIKINKU TO HAKIKA SHIMA YANA CIKINSU. HAKIKA ALLAH BA YA SHIRIYAR DA MUTANE AZZALUMAI". (Ma'idah ayah ta 51). Ibnu Abi Hatam ya

ANNABI MASOYIN AL'UMMARSA (SAWW).

``` Hakika in dai zamuyi adalci, to tabbas babu wanda ya kamata muso shi, Mu bishi, mu girmamashi, Mu kambama shi, Kamar Manzon Allah (saww). Shi ya kamata Muyi soyayya don soyayyarsa, Muyi kiyayya don kiyayyarsa kamar yadda Allah yake yi. Domin babu wanda yasomu, ya damu da sha'aninmu, Kuma yake tausayinmu Kamar Annabi Muhammadu (saww). Zan kawo wasu Misalai daga cikin irin soyayyarsa da kulawarsa garemu kamar haka : 1. Lokacin da Kafirai suka matsa wajen chutar dashi da mabiyansa, an nemi alfarma agareshi cewa ko zai yi addu'a irin wacce Annabi Nouhu (as) yayi, sai yace "A'a. Ya Allah ka shiryi Mutanena. Domin su basu sanni bane". Kunga da ache yayi waccan addu'ar, da tuntuni mun hallaka. To amma da yake shi BIL MU'UMINEENA RA'UUFUN RAHEEMUN ne, sai bai yi haka ba. Yayi mana alkhairin da babu iyaka. 2. Lokacin fitar rai, kowa ya san cewar mutum ba ya iya tunawa da kowa awannan lokacin. Ta kansa yakeyi. Amma Manzon Allah (saww) bai manta damu ba.

LABARIN WANI MAI ƘIN MUTUWA

Akwai wani saurayi mai tsananin ƙin mutuwa. Ba ya son jin ambatonta ko kuma ganin wani abu game da ita. Saboda tsananin ƙiyayyar da yake yiwa mutuwa, shi yasa ba ya zuwa gaisar da marar lafiya, Ba ya zuwa Jana'iza ballantana gaisuwar mutuwa (Wato Ta'aziyyah). Tun mutane basu gane halinsa ba, har dai suka fahimci yanayinsa. Abokansa ma sunyi masa nasiha akan haka amma sai ya rika kawo hujjoji marassa tushe domin kare kansa. Rannan dai sai gashi yayi aure, matarsa ta haifi yarinya mace. Wannan yarinyar ta taso cikin gata da kuma cikakkiyar kulawa daga mahaifinta. Wato yana sonta sosai. Ana nan, ana nan.. Rannan sai zazzabi ya kama wannan yarinyar. Kafin wani lokaci ta rasu. Mahaifinta (wato wannan saurayin) yayi tsananin bakin ciki sosai. Yayin da ya fito domin gayyatar mutane wajen jana'izarta akofar gidansa, sai yaga kamar mutane basu damu da mutuwar 'yarsa ba.... Duk inda yaje ya faɗa sai mutane suce "Allah ya jiƙanta" amma babu mai tasowa domin zuwa wa

HALAYEN MASU TSORON ALLAH (5)

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI. Salati da aminci da girma su tabbata bisa Annabin Rahama, Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa masu haske da sahabbansa masu albarka. Wannan shine kashi na biyar acikin darasinmu mai suna HALAYEN MASU TSORON ALLAH (SWT). Abubakar Ibnu Abi Shaibah ya ruwaito wani hadisi daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (rta) daga Manzon Allah (saww) yana cewa : "Ku karbi labari daga Banu Isra'eela babu makawa. Domin kuwa akwai abubuwan mamaki acikinsu". Sannan yaci gaba da bada labari yana cewa : "Wasu Jama'a (daga banu Isra'ila) sun fita zuwa wata makabarta, sai suka ce "Mai zai hana mu sallaci raka'a biyu sannan mu roki Allah ya fito mana da wani daga cikin Matattun nan domin ya bamu labari game da mutuwa!". "Sai suka aikata hakan. Nan take sai ga wani mutum ya fito da kansa ta cikin wani Qabari, ga gurbin sujadah nan yana yin haske atsakiyar goshinsa. Sai yace musu "Ya Ku wadan

MIRACLES OF PROPHET MUHAMMAD (SAWW)

https://youtu.be/IaJkuZ958uo

SAMFURIN HALITTAR DAN ADAM

Acikin kowanne Jima'i guda, mafi Qarancin Kwayoyin Maniyyin da suke fita daga jikin Namiji lafiyayye sun kai kamar kimanin guda Million Arba'in (40,000,000). Wani Namijin ma yakan fitar da sama da Million dari biyu da hamsin (250,000,000). Kowanne guda daya daga cikin wadannan Miliyoyin idan ya kyankyashe kwai za'a iya samun Mutum cikakke. To amma daga cikinsu din nan guda daya ne wanda Allah zai zaba ya samu shiga cikin Kwan halittar mace, daga nan kuma idan ya kyankyashe kwan sai su hadu su chure su zama gaurayen ruwan Maniyyi wanda shi ake kira "NUTFAH", wanda daga gareshi aka halicceka. Imamul Lalka'eey ya fitar da hadisi tare da isnadinsa mai inganci har zuwa Kan Sahabin Manzon Allah (saww) mai suna Sayyiduna Abdullahi bn 'Amru bn Al-Aas (rta) yana cewa: "Idan gaurayeyyen ruwan Maniyyi ya zauna acikin Mahaifar mace har tsawon kwana arba'in, Sai wani Mala'ika yazo gareta ya dauketa (ita nutfar) ya girgizata sannan ya tafi da ita zuwa ga

A KOWANNE HALI KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA TARA :

1. Duk lokacin da wata ni'ima ta sameka, ka gode ma Allah kafin ka gode ma kowa. Kace "ALHAMDULILLAH". 2. Duk lokacin da wata musibah ta sameka, Ka zargi kanka Kar ka zargi kowa. Kuma kace "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN". 3. Duk lokacin da Qofofin samunk suka toshe, to lallai sai ka tuno da yawan zunubinka. Ka yawaita ASTAGHFIRULLAH". 4. Duk lokacin da al'amura suka rinchabe maka, ko kuma Makiya suka sawoka gaba, Komai girman abun bai fi Qarfin Allah ba.  Don haka ka yawaita "LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BIL-LAAHIL ALIYYIL 'AZEEM". 5. Duk lokacin da Bakin ciki ya dameka, ko kuma bukatunka suka toshe, to ka yawaita Salati ga fiyayyen Halittu (saww) domin salatinsa yana haskaka zuciya, yana yaye damuwa, yana kawar da bakin ciki. 6. Duk lokacin da kaji zuciyarka ta bushe ta kekashe, (Babu tsananin taushin nan na tsoron Allah) To ka yawaita karatun Alqur'ani. Domin shi karatun Alqur'ani tare da Tadabburi (zurfafa tunani) c

GASKIYA SAHABBAI SUNJI DADINSU!

Hakika Sahabban Manzon Allah (saww) mutane ne wadanda babu irinsu. Sun fi dukkan Mutane daraja. Don banda Annabawa babu wanda yafisu daraja awajen Allah daga cikin mutane. Sun zauna da Annabi (saww) sunso shi, sun bishi, sun taimakeshi da dukiyoyinsu da rayukansu. Sun sayar ma Allah dukiyoyinsu da rayukansu. Shi kuwa ya saya ya biyasu da tukwuicin gidan Aljannah da kuma yardarsa ta har abada. Sun samu lambobin girmamawa daga Allah da Manzonsa (saww). # Shin yaya Sayyiduna Abubakrin yaji acikin zuciyarsa yayin da Manzon Allah (saww) yace masa : "DA ACHE ZAN RIKI BADA'DI ACIKIN MUTANE, TO DA NA RIKI ABUBAKAR AMATSAYIN BADA'DINA". # Shin yaya Sayyiduna Umar Al-Faruk yaji acikin zuciyarsa, alokacin da ya nemi izinin shigowa wajen Manzon Allah (saww) sai yace "KACE MASA YA SHIGO, KUMA KAYI MASA ALBISHIR DA SAMUN ALJANNAH". Kuma yace "ALLAH YA SANYA GASKIYA AKAN HARSHEN UMARU DA ZUCIYARSA". # Shin yaya Uthman Dhun Nurayni yaji azuciyarsa, bayan ya

KU DUBI IRIN WANNAN SOYAYYAR

Bayan an dawo daga Yakin Uhudu, kasancewar shine Yaqi na farko wanda Musulmai da yawa sukayi shahadah, Sai garin Madeena ya cika da kururuwar Mata da Qananan yara. Yayin da Manzon Allah (saww) yaji wasu mata daga dangin Banu Abdil-Ash'hal suna ta rusa kuka saboda mamatansu, Sai hankalinsa ya tashi. Ya tuna da Baffansa wato Sayyiduna Hamzah bn Abdil Muttalib (rta). Sai yace: "SAI DAI KUMA SHI HAMZA BASHI DA MASU YI MASA KUKA". Daga jin wannan Qaulin sai gaba daya Matayen mutanen Madeenah suka taho suka zauna suka fara rusa kuka domjn su taya Manzon Allah (saww) bakin cikin rabuwa da Baffansa. Suna ta kuka cikin dare har Manzon Allah (saww) yayi barci. Yayin da ya farka yaji har yanzu suna tayi, sai yace: "Ya Kaitonsu, har yanzu suna zaune anan? Ku umurcesu su koma (gidajensu) Kuma bayan wannan ranar kar su sake yin kuka bisa wani Mamaci". ADUBA : - ÃLUL BAITI HAULAR RASOOL (shafi na 101). - SUNANU IBNI MAAJAH (hadisi na 1591). Zauren Fiqhu, wannan yana n

ZUWA GA MASOYIN RAINA (SALLAL LAAHU ALAIHI WA AALIHI WA SALLAM)

Amincin Allah ya tabbata agareka gwargwadon matsayinka awajen Ubangijinka Ya Masoyin Allah. Hakika Ni na shaida cewa Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma shi kadai ya chanchanta a bauta masa. Kuma na shaida Kai Bawansa ne kuma Manzonsa ne. Ya aikoka alokacin da dukkan wani hasken shiriya ya riga ya dusashe. Gaskiya tayi Qas, sai Qarya take hankoro. Kazo da haskenka ka kauda dukkan Qarya da ma'abotanta. Ka isar da aiken Allah, Ka karya Gumaka ka tsarkake Bautar Allah. Ka fidda bayi daga Kafirci zuwa ga Imani, daga jahilci zuwa ga Ilimi, daga Zalunci zuwa ga adalci. Hakika na shaida cewa cikin dukkan bayin Allah babu tamkarka babu kamarka. Kai ne Shugaban dukkan bayin Allah. Kai ne Haskensu kuma da kai Allah ya haskakasu. Kai ne Shugaba kuma jagoran dukkan Annabawa da Manzannin Allah. Kuma kai kadai ne wanda saboda kai Allah ya tara dukkan Annabawa da Manzanni sai da sukayi Imani dakai, Suka dauki alkawarin cewa su Mataimakanka ne, zasu taimakeka akan aikinka sanna

KU DUBI WANNAN BAIWA

Image
Sayyiduna Naufal bn Al-Harith bn Abdil-Muttalib (rta)  ya nemi taimako awajen Manzon Allah (saww) alokacin da zai yi aure. (Mahaifinsa yayan Mahaifin Manzon Allah ne). Sai Annabi (saww) ya aura masa wata Mace. Bayan nan sai ya zamanto babu abinda zai ci. Don haka sai Manzon Allah (saww) ya aiki su Abu Rafi'in da Abu Ayyub Al-Ansariy (rta) suka jinginar da wasu kayan Yakinsa awajen wani Bayahude. Suka karbo masa Mudu Talatin na sha'eer. Naufal (rta) yace "Bayan Manzon Allah (saww) ya bani wannan Mudu Talatin na sha'eer din, mun ci gaba da cinsa har tsawon rabin shekara (6 months) sannan da muka aunashi sai muka ganshi kamar yadda yake.  (Wato yana nan daidai kamar ba'a ta'ba ci daga gareshi ba). Da naje na gaya ma Manzon Allah (saww) sai yace mun "DA ACHE BAKA AUNASHI BA, DA SAI YA ISHEKA MUTUKAR KANA RAYE" (Wato da zai isheka kaci har karshen rayuwarka). Imamul Hakim ne ya ruwaito wannan Mu'ujizar acikin MUSTADRAK juzu'i na biyu shafi na 2

ANNABINA SHUGABANA MACECINA (SAWW)

Image
ANNABINA, MASOYINA (SAWW) SHINE : ***************************************** DHU QUWWATIN : Ma'abocin Qarfin jiki da Qarfin Hujjah. Annabin da shi kadai yaci nasarar da sauran Annabawan Allah vasu samu ba. Ya kori shirka,  ya karya gumaka, ya tsarkake Ka'abah. DHU HURMATIN : Ma'abocin alfarma aduniya da lahira. Annabin da saboda shi Allah yake dauke Bala'i, kuma yake saukr da niimah.  Shine wanda saboda alfarmarsa al'ummarsa ta samu daukaka da darajoji. DHU MAKANATIN : Ma'abocin Qurewar Matsayi afadar Allah. Shine wanda Allah ya tara dukkan Annabawa sukayi imani dashi, sukayi masa chaffa, Suka dauki alkawarin taimakonsa wajen isar da sako. DHU 'IZZIN : Ma'abocin Buwaya aduniya da lahira. Shine wanda ya chusa tsoro da razana azukatan Sarakunan duniya tun afarkon lokacin bayyanarsa. DHU FADHLIN : Ma'abocin Falala da fifiko a saman dukkab halittu. Shine wanda ambaton sunansa yake yaye damuwa ga Masoyansa. Kallon fuskarsa yakan Gigita hankali,  Tun

LIKITAN LIKITOCI (SAWW)

Hadisi daga Sayyiduna Hubaibu bn Fuwaik (rta) yace: "Hakika Mahaifina ya tafi wajen Manzon Allah (saww) alhali alokacin nan idanuwansa sunyi fari fat baya ganin komai dasu. (Wato ya riga ya makance). Da Manzon Allah (saww) ya tambayeshi "MENENE YA SAMEKA?". Sai yace "Na kasance ina horar da Rakumina, Sai Qafata ta taka wani Qwai, Sai (ruwansa) ya zuba a idanuwan". Nan take da Annabi (saww) yayi masa tofi acikin idanuwansa sai ya fara gani (Wato ya warke tarwal). Ni na ganshi (shi Mahaifina) yana iya shigar da zare cikin allura, alhali alokacin nan yana ɗan shekaru Tamanin (80) aduniya, Kuma idanuwan nasa suna nan fari fat ɗin". ADUBA : DALA'ILUN NUBUWWAH na Baihaqiy, juzu'i na 6 shafi na 173. Wannan yana nuna mana tsantsar Mu'ujizah irin ta Ma'aikin Allah (saww). Da kuma tausayawarsa ga Sahabbansa (rta). Masu ilimin kiwon lafiyar jikin 'Dan Adam sun tabbatar da cewa dole sai da wannan ɗigon baƙin na cikin idanu sannan mutum zai i

ZAKKAR FIDDA KAI (PART ONE)

Image
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Tsira da aminci su Qara tabbata abisa fiyayyen halittu, Annabi Muhammadu da Iyalan gidansa da dukkan sahabbansa. Kamar yadda muka alkawarta, -INSHA ALLAHU zamu fara ne da kawowa hadisai wadanda suka yi magana akanta, tare da sharhi, sannan kuma daga baya mu leka wajen maluman fiqhu domin muji hukunce-hukuncen da suka fitar daga cikin wadannan hadisan: ★ HADISI NA FARKO: daga IBNU UMAR (rta) yace: "Manzon Allah (saww) ya farlanta zakkar fidda kai, Sa'i daya na dabino, ko Sa'i daya na sha'eer. Abisa kowanne bawa, ko 'da, da namiji ko mace, Qarami da babba daga cikin musulmi. Kuma yayi umurni abayar da ita kafin tafiya sallar (eedi)" (Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi) Wannan hadisin dalili ne akan wajibcin zakkar fidda kai, saboda cewar sa "YA FARLANTA". Domin hakan yana nufin ya lazimta, ya wajibta, Kuma ana fitarwa ne akan yaro da babba, Mace da namiji. Dukkan maluman fiqhu sunyi ittifaki akan

WACECE NANA FATIMAH?

AN HAIFI S AYYIDAH FATIMAH (A.S) acikin garin Makkah, ranar 20 ga watan Jumaada akhir, ashekara ta biyar bayan Manzanci. Wato shekara 8 kafin hijra. (kamar yadda yazo acikin "SIYARU A'ALAMIN-NUBALA'I. Ta taso cikin kyakkyawar tarbiyyah wacce babu kamarta. Kasancewar Mahaifiyarta ita ce Nana Khadeejah bintu Khuwailid (rta) wacce ta zamto Mafificiya acikin Matayen Zamanin da, harma na yanzu. Mahaifinta kuwa shine Shugaban dukkan Annabawa da Manzanni (saww). Kuma shine mafificin halittu ta wajen kyawun hali da dabi'u. Nana Fatimah fara ce kyakkyawa mai kyawun diri. Tafi kowa daukar kamannin mahaifinta. Tayi kama dashi wajen zamansa da tashinsa da tafiyarsa da maganarsa da murmushinsa. Nana Fatimah ta taso da kaifin hankali da basira wacce ta zarce sauran tsararrakinta. Don babu tamkarta acikin Matayen zamaninta. Ta kasance tana taimakon mahaifinta wajen isar da sakon Allah, Kuma duk da kasancewarta yarinya Qarama alokacin, takan nuna fushinta akan abinda kafirai suk

FIQHUN AZUMI DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (13)

FIQHUN AZUMI DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (13) BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Allah kayi salati irin naka abisa Shugaban Manzanninka, kuma Jagoran Halittunka, Annabinmu Muhammadu tare da Iyalan gidansa Tsarkaka da Sahabbansa Madaukaka. Awancan karatunmu wanda ya gabata, munyi magana akan abubuwan da suke Karya azumi amma bangaren wadanda suke wajabta ramuko ba tare da kaffara ba. Yanzu kumq insha Allahu zamu shiga bangaren wadanda suke karya Azumi kuma suke wajabta Ramuko da kuma Kaffara gaba daya. ★ JIMA'I shine abinda yake warware azumi, kuma yake wajabta Qadha'i  tare da kaffarah. Saboda hadisin da Bukhary da Muslim da Abu Dawud da Ahmad da Tirmizy suka ruwaito daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra): "Wani mutum yazo wajen Manzon Allah (saww) sai yace masa: "YA RASULALLAHI NA HALLAKA!!" Sai Annabi (saww) yace masa "MENENE YA HALLAKAR DAKAI?". Sai yace "Na afkawa Matata acikin Ramadhana!!". Sai Manzon Allah (saww) yace masa "SHIN KANA D

FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW)

Farkon wanda zai shiga Aljannah aranar Alqiyamah shine Annabinmu Muhammadu (saww) kamar yadda Imamu Muslim ya ruwaito daga Sayyiduna Anas bn Malik (rta) yace Manzon Allah (saww) yace: "ZAN ZO KOFAR ALJANNAH ARANAR ALQIYAMAH, SAI IN KWANKWASA, SAI MAI TSARONTA (WATO MALA'IKA RIDHWAN) YACE : "KAI WANENE?". ZAN CE MASA "MUHAMMADU NE". SAI YACE : "SABODA KAI AKA UMURCENI KAR IN BUDE MA WANI KAFIN KA". Acikin wata ruwayar kuma yace: "NINE NAFI DUKKAN ANNABAWA YAWAN MABIYA, KUMA NINE FARKON WANDA ZAI KWANKWASA (KOFAR ALJANNAH)." (Muslim ne ya ruwaitoshi). Acikin ruwayar Abu Hurairah kuma Annabi (saww) yace: "MUNE NA KARSHE KUMA MUNE NA FARKO ARANAR ALKIYAMAH. KUMA MUNE FARKON WADANDA ZASU SHIGA ALJANNAH". (Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi). Akwai kuma hadisan da suka nuna cewar Talakawan wannan al'ummar sai sun riga mawadata (Masu kudi) shiga Aljannah, kamar yadda Imamu Ahmad da Tirmidhiy suka ruwaito Daga Sayyiduna A

MATA FITINAR DUNIYA

MATA FITINAR DUNIYA ************************* "YANA DAGA CIKIN AYOYINSA, YA HALICCI MATA DAGA GAREKU, DOMIN KU SAMU NUTSUWA ZUWA GARESU, KUMA YA SANYA SOYAYYA DA TAUSAYI ATSAKANINKU. HAKIKA ACIKIN WANNAN AKWAI ABIN LURA GA MUTANE MASU TUNANI". Acikin wannan ayar Allah ya bayyana mana ainihin dalilin da yasa ya halicci mata daga garemu kuma ya sanya suka zama abokan zamanmu. Acikin wata ayar kuma yace: "YA KU MUTANE KUJI TSORON UBANGIJINKU WANDA YA HALICCEKU DAGA RAI KWAYA 'DAYA, KUMA YA HALICCI ABOKIYAR ZAMANTA DAGA GARETA, KUMA YA FITAR DA MAZAJE MASU YAWA GARESU DA KUMA MATAYE". (Suratun Nisa'i ayah ta 1). Ibnu Katheer ya rubuto acikin littafin Tafseer dinsa cewa "Yayin da Annabi Aadam (as) yake barci agidan aljannah akan ciri Qashin Hakarkarinsa na dama, aka halicci Nana Hauwa'u dashi. Yayin da ya farka daga barcinsa, ya ganta kuma ya samu nutsuwa daga gareta, itama ta samu nutsuwa daga gareshi. Amma lokacin da Iblees (L. A) yazo domin ya

HADISINMU NA YAU (03 GA RAMADHAN 1437)

Hadisin namu na yau yana kunshe da wata Qissah ce mai ratsa jiki. An karboshi daga Sayyiduna Abu Sa'eed Al-Khudriy (Malik bn Sinaan) Allah shi yarda dashi. Shi kuma ya karbo daga Manzon Allah (saww) yace: "Ya kasance acikin al'ummar da suka gabaceku akwai wani mutum wanda ya kashe Rayuka guda Chasa'in da tara (99). Sai yayi tambaya cewa (Yana so a nuna masa) Mutumin da yafi kowa Ilimi adoron Qasa, sai aka nuna masa wani Mutum mai bautar Allah. Sai ya Qarasa wajensa yace masa Shi ya kashe rayuka guda 99. Shin (Allah) zai karbi tubansa kuwa?". Sai wannan mai bautar Allah din yace masa "A'a". Don haka sai ya kasheshi ya cika 'dari (100) dashi. Sannan sai ya sake tambaya akan anuna masa Wanda yafi kowa Ilimi adoron Qasa. Sai aka nuna masa wani Mutum Malami. Sai ya gaya masa cewa Shi ya kashe rayuka guda 'dari (100). Shin za'a karbi tubansa kuwa?. Sai Malamin yace masa "Kwarai kuwa. Waye ya isa shiga tsakaninsa da tsak

CIKIN QABARIN MUMINI

Ranar da aka sanya Mumini cikin Qabarinsa, rana ce mafi Muhimmanci gareshi. Rana ce wacce zai fita daga gidan wahala da Qunci da bakin ciki (wato duniya). Zai koma zuwa ga gidan hutu da yalwa da farin ciki. Rana ce wacce Mumini zai fara girbar alkhairin da ya shuka.. Wato sallolinsa da azuminsa da sadakokinsa da Zikiransa wadanda ya gabatar. Rana ce wacce Ubangijinsa zai cika masa alkawarin da yayi masa.. Wato Alkawarin cewa zai, shigar dashi cikin ni'imarsa mutukar dai yayi imani kuma ya aikata ayyuka na Kwarai. Rana ce wacce zai rabu da danginsa da iyalansa da dukiyoyinsa, Zai shiga cikin Ni'imar Ubangijinsa, da kuma arzikin da ba ya Qarewa. Rana ce wacce Mumini zai chiza yatsansa, yana burin inama za'a bashi damar dawowa duniya domin ya aikata wasu Qarin ayyukan alkhairi. Saboda irin girmamawar da ya samu awajen Ubangijinsa. Rana ce wacce dukkan 'Yan uwansa da danginsa suna cikin Kuka, da Bakin ciki. Amma shi kuwa yana cikin farin ciki da annashuwa. Wasu daga

CIKIN QABARIN MUMINI

Ranar da aka sanya Mumini cikin Qabarinsa, rana ce mafi Muhimmanci gareshi. Rana ce wacce zai fita daga gidan wahala da Qunci da bakin ciki (wato duniya). Zai koma zuwa ga gidan hutu da yalwa da farin ciki. Rana ce wacce Mumini zai fara girbar alkhairin da ya shuka.. Wato sallolinsa da azuminsa da sadakokinsa da Zikiransa wadanda ya gabatar. Rana ce wacce Ubangijinsa zai cika masa alkawarin da yayi masa.. Wato Alkawarin cewa zai, shigar dashi cikin ni'imarsa mutukar dai yayi imani kuma ya aikata ayyuka na Kwarai. Rana ce wacce zai rabu da danginsa da iyalansa da dukiyoyinsa, Zai shiga cikin Ni'imar Ubangijinsa, da kuma arzikin da ba ya Qarewa. Rana ce wacce Mumini zai chiza yatsansa, yana burin inama za'a bashi damar dawowa duniya domin ya aikata wasu Qarin ayyukan alkhairi. Saboda irin girmamawar da ya samu awajen Ubangijinsa. Rana ce wacce dukkan 'Yan uwansa da danginsa suna cikin Kuka, da Bakin ciki. Amma shi kuwa yana cikin farin ciki da annashuwa. Wasu daga

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (043)

CIKAWA DA KYAKKYAWAN AIKI ********************************** Hadisi daga Huzaifah Ibnul Yamaan (rta) yace : "Na shiga wajen Manzon Allah (saww) alokacin jinyarsa wacce ya rasu acikinta. Sai yace "ZAUNAR DANI". Sai Sayyiduna Aliyu (ra) ya zaunar dashi ya jinginar dashi zuwa ga Qirjinsa. Sai nace ma Aliyu din "Ya Abu Hamza, Ka kwana kana jinyarsa (wato ina so nima ka barni inyi jinyar Manzon Allah). Sai Manzon Allah (saww) yace: "YA KAI HUZAIFAH, AI ALIYU YAFI KA CHANCHANTA DA WANNAN AIKIN..  MATSO NAN KUSA DANI". (Da na Matso kusa dashi sai yace). "YA HUZAIFAH! DUK WANDA "LA ILAHA ILLAL LAAHU" TA ZAMANTO AIKINSA NA KARSHE KAFIN MUTUWARSA, TO ZAI SHIGA ALJANNAH. KO KUMA ZA'A GAFARTA MASA. "YA HUZAIFAH! DUK WANDA AKA CIKA MASA (AIKINSA NA KARSHE) KAFIN MUTUWARSA DA AZUMIN RANA GUDA DOMIN NEMAN YARDAR ALLAH, ZAI, SHIGA ALJANNAH, KO KUMA ZA'A GAFARTA MASA". "YA HUZAIFAH! DUK WANDA AKA CIKA MASA AIKINSA NA KARSHE KAF

HUKUNCIN MASU SAIDA SIGARI DA KAYAN MAYE

TAMBAYA TA 1934 ******************** ASSALAMU ALAIKUM MAL DON GIRMAN ALLAH A'ANSA MIN TAMBAYA. YAYA HUKUNCI MAI SAYAR DA SIGARI DA KWAYOYIN SA MAYE A MUSULINCI? NAGODE ALLAH YAKA DA ALHERI AMIN DAGA DALIBINKA SHAFIU BELLO ANKA ZAMF WASSALAM AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Duk abinda amfani dashi ya zama Haramun, to hakanan sayar dashi ko dakonsa ko shukawa, ko girbewa ko sarrafawa duk HARAMUN ne. Kuma dukkan abinda ke sanya maye, sunansa giya ne. Kuma Allah ya haramta giya, ya kuma tsine ma masu yinta da masu dakonta da masu shayar da ita da masu sayar da ita. Ita kuwa Sigari kayan Almubazzaranci ce. Kuma Allah yace su Amubazzarai 'Yan uwan shaitan ne. Shi kuwa shaitan ya butulce ma Ubangijinsa ne. Hukuncin mai sayar da irin wadannan abubuwan shine ya aikata HARAM. Domin kuwa Allah yace "KUYI TAIMAKEKENIYA BISA BIN ALLAH DA KUMA TAQWA. KADA KUYI TAIMAKEKENIYA CIKIN SA'BON ALLAH DA QETARE IYAKOKINSA". Sayar da Sigari da kay

BASU SON 'YARSU TA AURI TALAKA

TAMBAYA TA 1928 ******************** Assalamullahi alaika, Allah y qara lpy d rayuwa mai ampani. amin. mallam dan Allah ataimaka mun da addu'ar dazan dunga yi. Mun kasance muna son juna d saurayina, kuma aure ya kawoshi. Amma wadanda nake zaune awajensu basa so wai saboda malamin makaranta ne har sukancemin wai "me nasama yaci bare yaba naqasa" Ni kuma nafi son yin auren kwanciyar hankali da ganin mutuncin juna koda kullum sai ya fita zai samo. Dan Allah mallam ataimaka mun da addu'ar dazan keyi kan Allah ya Fahimtar dasu su goya mun baya. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Abinda zakiyi da farko shine Ki dogara ga Allah, domin duk wanda ya dogara ga Allah sai Allah din ya isar masa akan dukkan damuwarsa. Ki yawaita yin addu'ar nan ta Annabi Yunus (as) wacce Manzon Allah (saww) yace "BABU WANI WANDA YAKE CIKIN BAKIN CIKI DA ZAI KARANTA-TA FACHE SAI ALLAH YA YAYE MASA". Addu'ar ita ce "LA ILAHA ILLA ANTA SUBHAN

SAYYIDUNA ABUBAKRIN (RTA) -3

KHALIFAN MANZON ALLAH (saww) Azamanin Khalifancinsa, bayan wafatin Manzon Allah (saww) Farkon annobar data fara kunnowa kai ita ce: RIDDA da yawancin larabawan Qauyuka suka rika yi. Mafiya yawansu daga jin cewar Manzon Allah (saww) yayi wafati shikenan sai sukayi ridda suka fice daga Musuluncin. Wasu kuma basu bayyana cewar sun fita daga Musuluncin ba, sai dai sun Qi bayar da zakkah. Wasu kuma bayan riddar ma, har sun fara da'awar Annabta. Irinsu Musaylamah Alkazzab. Har sai da ya zama iya garuruwa 3 ne kadai ake yin Musulunci aduniya. Wato Makkah, Madeenah, da Ta'if. Amma matakin farko da ya fara yi shine zartar da abubuwan da Manzon Allah (saww) ya riga ya fara su. Misali kamar tashin rundumar Usamah bn Zaid bn Harithah zuwa yakin Rum. Da yawa daga cikin Sahabbai sunyi niyyar hanashi tura wannan rundunar. Saboda ganin halin da ake ciki. Yayin da Sayyiduna Umar (ra) ya tareshi ya gaya masa cewar bai kamata atura wannan rundunar ba. Sai ya bada amsa cewar: "Walla

FALALAR NEMAN ILIMI

Mafiya yawan mutanenmu awannan zamanin basu dauki neman ilimin addini amatsayin da ya kamata su daukeshi ba. Sun daukeshi ne amatsayin wani abu na wucin-gadi. (Wato kamar bai zama lallai akansu ba). Manzon Allah (saww) yace "NEMAN ILIMI FARILLA NE AKAN KOWANNE MUSULMI DA MUSULMA". Ilimi yana sama da dukkanin wata baiwa wacce Allah yake yiwa 'Dan Adam. Shi yasa ma Allah ya umurci Annabinsa (saww) cewa ya rika yin addu'ar neman Qarin ilimi yana cewa : "KACE YA UBANGIJI KA QARA MIN ILIMI". Sannan tun farko wannan jinsin namu ya samu daukaka ne saboda albarkar ilimi. Allah ya Umurci Mala'iku sunyi Sujjadah ga Annabi Aadam (as) ne saboda fifikon ilimin da yayi musu. Ilimin addini abu ne wanda ya zama Wajibi ka nemeshi tun daga zanin goyo, har zuwa Qabarinka. Babu ranar denashi. Domin kuwa idan kaje ma Allah amatsayinka na jahili, to fa baka da sauran wani uzuri awajensa (SWT). "Ban sani ba" ko kuma "Ban samu lokaci ba" Ba zasu zama Uz

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ************************************** Anan ZAUREN FIQHU Muna yawan samun tambayoyi akan wannan Mas'alar daga bangarorin Maza da mata. Amma in sha Allahu yanzu zanyi bayani daidai gwargwadon iko. Bismillahir Rahmanir Raheem. Ina fatan zaku gafarceni. Zanyi bayani dalla dalla (duk da cewar akwai nauyi sosai) to amma abu ne wanda ya shafi addini. Kuma bangaren tsarki ne wanda sai dashi ibadah zata yiwu. Maniyyi da Maziyyi suna da bambanci ta bangarori guda uku kamar haka: 1. Bambanci a yanayin Siffarsu. 2. Bambanci ayanayin da ake ji bayan fitarsu. 3. Bambanci a bangaren hukuncinsu. 1. SIFFOFINSU ***************** Manzon Allah (saww) shi da kansa yayi bayanin yadda siffarsu take yayin da yake bada amsa bisa tambayar da Sayyidah Ummu Sulaym tayi masa. Yace : "SHI DAI MANIYYIN NAMIJI, FARI NE KUMA YANA DA KAURI. SHI KUMA MANIYYIN MACE, FATSI FATSI NE, KUMA TSINKAKKE NE (BASHI DA KAURI). (Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi). Akan wannan n

DALILAN DAKE JANYO MA MUTUM AZABAR QABARI

Kwanciyar Qabari tana daga cikin manyan Jarrabobin dake jiran kowanne mutum dake raye aduniyar nan. Kowa zai fara riskar yanayin sakamakon ayyukansa ne tun daga Qabarinsa. Kamar yadda muka bayyanar acikin Lakchochinmu da dama wadanda muka gabatar anan Zauren Fiqhu, lallai Hadisai sun tabbata daga Manzon Rahama (saww) wanda ya tabbatar da cewa Shi Qabari shine Masauki na farko daga Masaukan Lahira. Idan yayi kyau, to abinda ke gabansa ya fishi kyawu. Idan kuma yayi Muni, to abinda ke gabansa ya fishi Muni. Kuma lallai duk inda kaga Qabari, to kodai ya zamanto dausayi ne daga dausayoyin Aljannah, ko kuma Kwazazzabo ne daga Kwazazzaban azabar wutar jahannama. Kuma lallai babu bambanci cikin adadin dadewar da bayin Allah zasuyi acikin Qabarinsu. Da wanda ya mutu tun azamanin farko, da wanda ya mutum awannan zamanin da muke ciki, duk babu bambanci. Hakanan babu bambanci tsakanin wanda ya mutu aka binneshi, da wanda ya mutu acikin ruwa gawarsa ta ru'be, da wanda wuta ta cinye namansa,