Posts

Showing posts from 2019

MAI MATSAYIN QUREWA (SAWW).

Manzon Allah (saww) shine cikakken Malamin al'ummah. Malamin da bai koyi karatu awajen kowa ba, amma awajensa kowa yake kwankwadar ilimi. Acikin maganganunsa zaka samu Ilimai na zahiri da na 'boye. Zaka ji Ilimin Geography, Physiology, Astrology, Gynaecology, Botany, Economy, da sauran dubban ilimai wadanda babu wani 'Dan Adam da ya sansu. Allah ya fifita Annabi Aadamu akan Mala'iku ne tunda ya san ilimin Sunaye wanda su basu sani ba.. Don haka Allah yace suyi masa Sujadah su gaisheshi. Shi kuwa Annabi Yusufu (as) Allah ya fifitashi akan sauran 'Yan uwansa ne da ilimin sanin fassarar Mafarkai da kuma Mafita acikin al'amura boyayyu. Don haka Allah ya bashi Mulki da fifiko asamansu. Shi kuwa Khidru (as) Allah ya sanar dashi wani ilimi ne tsakaninsa dashi, ba tare da wani atsakani ba.. Ya sanar dashi Ilimin hangen nesa. Don haka ma ya bashi Manyan Annabawa suka zama Almajiransa. Wato irin su Annabi Musa da Yusha'u (alaihimus Salam). Annabi Dawud Allah ya s

MU SAN ANNABINMU (31)

Da sunan Allah mamallakin dukkan komai, Salati da amincinsa su tabbata bisa Fiyayyen Annabawansa, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa madaukaka, da masu biye dasu da dukkan Salihan bayi har zuwa ranar sakamako. Sannan shine kashi na talatin da daya acikin darasin tarihin Ma'aiki (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) wanda ke zuwa daga Zauren Fiqhu Whatsapp. Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya. Idan baku manta ba, a darasinmu na 30 mun tsaya ne akarshen bayanin abubuwan da suka faru a yaqin gwalalo. Yanzu kuma zamu shiga cikin bayanin   yaqin da akayi da Yahudawan Banu Quraizah wadanda suka hada baki da kafirai don yaqar musulmai. YAQIN BANU QURAIZAH ************************* Yayin da Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya wayi gari sai ya koma cikin garin Madeenah tare da sauran jama'ar musulmai duk suka ajiye kayan yaqinsu (wato makamai). Shi kuwa Sayyiduna Sa'adu bn Mu'az (radhiyallahu anhu) saboda damuwa d

MU SAN ANNABINMU (30)

Da sunan Allah Sarkin Sarakuna, Salatai marassa yankewa su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa da Sahabbansa tare da aminci gwargwadon girmansa. Wannan shine kashi na talatin acikin darasin tarihin Shugaban halittu (saww) wanda ke zuwa daga Zauren Fiqhu. Kuma zamu dora daga inda muka tsaya ne acikin bayanin yaqin gwalalo (Gazwatul Ahzab). Yayin da wannan sahabi (Sa'adu bn Mu'az) ya samu wannan mummunan rauni sai yai addu'a ga kafirai da yahudawan da sukayi yaudara, yace: "Ya Allah idan har akwai abinda ya saura daga yaqin Quraishawa, to ka wanzar dani (in halarci yaqin) domin babu wasu mutanen da nafi so in yaqesu fiye da wadannan da suka chutar da Annabinka kuma suka Qaryatashi. To Ya Allah idan kuma ka kawar da yaqi atsakaninmu dasu, to ka sanya (wannan raunin da akayi mun) ya zamto shahada gareni, kuma kada ka kasheni har sai ka faranta mun raina game da yahudawan banu quraizah". To dama su Banu Quraizah sun kasance abokan huldarsa ne kuma maji

MADUBIN DUBAWA (75)

QARSHEN MAI CI DA ADDINI ***************************** Al Imam Ibnul Jauzee ya hakaito daga Uthman bn Abdillah cewa a zamanin Annabi Musa (amincin Allah ya tabbata gareshi da Annabinmu) akwai wani mutum wanda yake hidimta masa, kuma yana neman ilimi awajensa. Watarana sai wannan mutumin ya nemi izini awajen Annabi Musa (alaihis salam) cewa yana so zai je garinsu ya dawo. Sai Annabi Musa (alaihis salam) yayi masa izini ya tafi. Amma daga zuwansa sai ya mayar da kansa tamkar shine malamin garin. Yana tashi yana wa'azi atsakanin mutanen garin, motsi ka'dan sai yace musu "Musa kaleemul Lahi (alaihis salam) ya bani labari cewa kaza yayi kaza". Ko kuma "Annabi Musa mai ganawa da Allah ya bani labari cewa kaza yayi kaza... ". Su kuma mutanen garin suna jin dadi suna tara masa dukiya har dai ya tara kudi da dukiya mai yawan gaske. Kuma daga nan ya zauna agarinsu bai sake komawa wajen Annabi Musan ba. Shi kuwa Annabi Musa (alaihis salam) ya kasance yana yawan t

MU SAN ANNABINMU (29)

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, Salati da amincinsa su tabbata bisa zababben zababbunsa Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya. Har yanzu dai muna cikin bayanin abubuwan da suka faru ne a lokacin yaqin Ahzab (yaqin gwalalo) wanda mushrikan Quraishawa suka ha'da kai da sauran Qabilun larabawa da yahudawa da munafukan madeenah domin su murkushe musulunci amma Allah bai idda nufinsu ba. Dakarun Mushrikan Makkah sunyi sansani atsakanin tudun nan mai suna Juruf da Zugabah, su kuma Qabilar Gatfan sunyi sansani kusa da dutsen Uhudu, Shi kuma Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya fito tare da Sahabbansa guda dubu uku sun yi nasu sansani kusa da dutsen Sal'u. Dama a baya na gaya muku cewa Yahudawan Madeena (wato Banu Quraizah) sun warware alkawarin dake tsakaninsu da Musulmai, don haka dole aka kwashe Qananan yara da Mata duk aka boyesu awani waje saboda tsoron sharrin Yahudawa. Ana cikin wannan tashin hankali

MU SAN ANNABINMU (27)

Da sunan Allah Mabuwayi Gagara-Misali,  Salati da amincinsa madawwama su tabbata bisa cikakken bawansa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya. Da mabiyansu da magoya-bayansu har zuwa ranar cikar alkawari. 'Yan uwa wannan shine fitowa ta ashirin da bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu Whatsapp mai dauke da tarihin rayuwar Ma'aikin Allah (saww). Mai taken "MU SAN ANNABINMU". Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya a darasinmu wanda ya gabata kamar haka : YAQIN BADAR NA KARSHE : Idan baku manta ba, aranar yaqin uhudu lokacin da Abu Sufyan yaga alamar kamar sune da nasara (Aun shahadantar da mutum saba'in daga cikin musulmai) sai yace : "Uhudu ramuwar badar ce. Kuma shekara mai zuwa mu hadu a badar". Don haka da shekara ta zagayo, wato acikin shekara ta hudu kenan bayan hijirah, sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi shirin yaqi ya fita zuwa filin nan na badar (wajen da akayi wa

MU SAN ANNABINMU (27)

Da sunan Allah Mabuwayi Gagara-Misali,  Salati da amincinsa madawwama su tabbata bisa cikakken bawansa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya. Da mabiyansu da magoya-bayansu har zuwa ranar cikar alkawari. 'Yan uwa wannan shine fitowa ta ashirin da bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu Whatsapp mai dauke da tarihin rayuwar Ma'aikin Allah (saww). Mai taken "MU SAN ANNABINMU". Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya a darasinmu wanda ya gabata kamar haka : YAQIN BADAR NA KARSHE : Idan baku manta ba, aranar yaqin uhudu lokacin da Abu Sufyan yaga alamar kamar sune da nasara (Aun shahadantar da mutum saba'in daga cikin musulmai) sai yace : "Uhudu ramuwar badar ce. Kuma shekara mai zuwa mu hadu a badar". Don haka da shekara ta zagayo, wato acikin shekara ta hudu kenan bayan hijirah, sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi shirin yaqi ya fita zuwa filin nan na badar (wajen da akayi wa

MU SAN ANNABINMU (27)

Da sunan Allah Mabuwayi Gagara-Misali,  Salati da amincinsa madawwama su tabbata bisa cikakken bawansa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya. Da mabiyansu da magoya-bayansu har zuwa ranar cikar alkawari. 'Yan uwa wannan shine fitowa ta ashirin da bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu Whatsapp mai dauke da tarihin rayuwar Ma'aikin Allah (saww). Mai taken "MU SAN ANNABINMU". Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya a darasinmu wanda ya gabata kamar haka : YAQIN BADAR NA KARSHE : Idan baku manta ba, aranar yaqin uhudu lokacin da Abu Sufyan yaga alamar kamar sune da nasara (Aun shahadantar da mutum saba'in daga cikin musulmai) sai yace : "Uhudu ramuwar badar ce. Kuma shekara mai zuwa mu hadu a badar". Don haka da shekara ta zagayo, wato acikin shekara ta hudu kenan bayan hijirah, sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi shirin yaqi ya fita zuwa filin nan na badar (wajen da akayi wa

TAFKIN AL KAUTHARA

TAFKIN ALKHAUTHARA Yana daga cikin manyan abubuwan ni'ima na lahira wadanda Allah ya tanadar wa Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) domin girmamawa gareshi da al'ummarsa. Acikin hadisai da dama Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi bayanin siffofin yadda tafkin yake, da kuma wadanda zasu sha daga gareshi. Misali hadisin Sayyiduna Abdullahi bn Umar (radhiyallahu anhuma) wanda yace Manzon Allah (saww) yace : "Tafkina (fa'dinsa) kamar nisan tsakanin Adanin da Amman, yafi Qankara sanyi, yafi zuma zaqi, kuma yafi dadin Qamshi fiye da Almiski. Kofunansa  kamar yawan taurari, wanda yasha daga gareshi ba zai Qara jin kishirwa ba har abada. Farkon mutanen da zasu fara gangarowa gareshi sune talakawan Almuhajirun. Sai wani yace "Su wanene Ya Rasulallah?!". Sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "Sune wadanda gashin kansu yake da Qura-qura, fuskokinsu suke dauke da alamar wahala, tufafinsu yana da d

MU SAN ANNABINMU (28)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa mafi daukaka Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu albarka, da dukkan salihan bayin Allah. Wannan shine darasi na ashirin da takwas acikin tarihin  rayuwar Manzonmu avin koyinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) kuma har yanzu dai muna bayanin yakokinsa ne, zamu dora in sha Allahu daga inda muka tsaya. YAQIN AHZAB : Wannan yaqin shi ake kira Yaqin gwalalo kuma ya faru ne acikin watan shawwal a shekara ta biyar bayan hijirah. Kuma yana daga cikin manyan yakokin da suka fi tada hankulan jama'ar Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) amma daga karshe Allah ya basu rinjaye da nasarori. Ga yadda abun ya faru kamar haka : Yahudawa sunyi nufin makirci da tayar da fitina ga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) don haka sai suka rika kwadaitar da mushrikan Quraishawa akan su fito su ha'da kai dasu tare da sauran Qa

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (122).

SHAYAR DA MAI RAI ********************* Hadisi daga Muhammadu 'dan Seerina, daga Sayyiduna Abu Hurairah (Allah ya yarda dashi) yace Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agareshi) yace : "WATARANA WANI KARE YANA ZAGAYE WATA RIJIYA, QISHIRWA TA KUSAN KASHESHI SAI WATA KARUWA DAGA KARUWAN BANU ISRA'EELA TA GANSHI. SAI TA CIRE TAKALMINTA (TA JANYO RUWA) TA SHAYAR DASHI, SAI AKA GAFARTA MATA SABODA WANNAN". ADUBA : Sahihul Bukhariy (juzu'i na 3 shafi na 1279). QARIN BAYANI *************** Tausayi yana daga cikin siffofin Ubangiji. Don haka Allah yana yin rangwame da afuwa da fifiko ga duk bawansa wanda ya siffantu da wannan siffar. Ku dubi girman laifin zina, musamman ga wacce ta maidashi sana'arta. Amma Allah ya gafarta mata saboda shayar da kare ruwa da tayi. To yaya kuma wanda ya shayar ko ya ciyar da Dan Adam, wanda darajarsa agun Allah tafi na kare!!. Yaku 'Yan uwa Musulmai! Mu Qara kokari mu sanya himma sosai wajen taimakon al'um

FALALAR ADDU'A DA MUHIMMANCINTA (FITOWA TA FARKO)

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI. SALATI da amincin Allah su tabbata ga zababben Allah, shugabanmu ANNABI MUHAMMADU, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansu yardaddu. In sha Allahu zamu dora gada wajen da muka tsaya ne acikin maganar FALALAR YIN ADDU'A DA KUMA MUHIMMANCINTA. Manzon Allah (saww) yace : "HAKIKA ALLAH MADAUKAKIN SARKI RAYAYYE NE, KUMA MAI KARAMCI NE. YANA JIN KUNYAR MUTUM YA CIRA HANNYENSA GARESHI, KUMA ACE YA DAWO DASU TA'BABBU BABU KOMAI AKANSU". (Sahihul Jaami'i). Kun ga wannan hadisin yana karantar damu cewa mu rika kyautata tsamaninnu ga Ubangijinmu. Lallai shi yana jin kunyar mu rokeshi bai amsa mana ba. Awani hadisin kuma Manzon Rahama (saww) yace: "IDAN DAYANKU ZAI YI ADDU'A, KAR YACE "ALLAH GAFARTA MIN IDAN KASO". LALLAI NE MUTUM YA SANYA MUHIMMANCI CIKIN ROKONSA, KUMA YA GIRMAMA KWADAYINSA, DOMIN SHI ALLAH BABU ABINDA YAFI GIRMAN BMYA BAYAR DASHI". (Sahihul Jaami'i). Shi kuma wannan hadisin ya

ADDU'AR MU TA YAU

Godiya ta tabbata gareka Ya Allah wanda cikin karamcinka da baiwarka ka sake nuna mana wani Ramadhan din bayan wani.. Ya Allah don tausayinka da jin Qanka ka bamu ikon aikata ayyukan alkhairi ka rabautar damu da samun yardarka matabbaciya. Ka kiyayemu daga sharrin zukatanmu da sharrin shaidan abin jefewa. Ya Allah ka azurtamu da biyayya gareka acikin wannan watan da bayansa, ka kiyayemu daga sa'ba maka acikinsa da bayansa. Ka sanyamu cikin bayinka wadanda taimakonka da agajinka ke tare dasu a ko yaushe, wadanda tuntube ko kuskure ba zai chutar dasu ba. Ya Allah ka sanyamu acikin mafiya samun mafi girman rabo daga duk wata rahama da gafara da baiwa da karamci da daukakar daraja, da falala da fifiko da kyauta wacce kake yiwa bayinsa awannan watan, Kuma ka sanyamu cikin jerin farko na bayinka da kake 'yantawa awannan watan. Ya Allah muna rokonka daga dukkan wani alkhairin da Manzonka kuma bawanka , Annabinmu Muhammadu ya ta'ba rokarka shi. Kuma muna neman tsarinka daga sha

MU SAN ANNABINMU (26)

Salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Acikin wannan darasin na Zauren Fiqhu zamu dora daga inda muka tsaya acikin tarihin Manzon Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). YAQIN HAMRA'UL ASAD : Washegarin dawowa daga yaqin uhudu sai Manzon Allah (saww) yayi tunanin watakil mushrikan Quraishawa su sake kawo hari garin madeenah don haka yayi nufin fita domin sake tararsu a sake wani sabon gumurzu don a nuna musu cewa har yanzu fa musulunci yana nan da Qarfinsa. Ashe kuwa shi Abu Sufyan shugaban dakarun Quraishawa ya daura niyyar dawowa din don Qara kawowa hari akan Musulmai, akan hanyarsa sai ya hadu da wani mutum mai suna Ma'abadu 'dan Ubayyu Alkhuza'iy. Sai Abu Sufyan din ya tambayeshi "Meye labarin abinda ke bayanka?". Sai yace masa "Ya kai Abu Sufyan, yi sauri ka guje daga garesu domin hakika sun tanadi makama

LABARIN CIKIN QABARI

Ibnu Abid Dunya ya ruwaito ta hanyar Hammadu bn Salamah, shi kuma ya karbo daga Hisham bn 'Urwah, shi kuma daga Babansa yana cewa : "Watarana wani mahayin doki yana tafiya atsakanin garin Makkah da Madeenah sai gashi kusa da wata Maqabarta,  sai yaga wani mutum ya fito daga cikin Qabarinsa yana ci da Wuta!!. Ga kuma Qarafuna an daddaureshi dasu. Sai yace "Ya kai bawan Allah! Hure min wutar nan! Hure min wutar nan!". Nan take sai ga wani ya sake fitowa ta cikin wannan Qabarin, yabi wancan din yana cewa "Ya kai bawan Allah kada ka bushe masa (wutar nan)!" Nan take shi wannan mahayin dokin ya suma akan dokin nasa. Kuma dokin yaci gaba da tafiya dashi ahaka har sai da ya kaishi wajen wata rijiya. Yayin da ya farka sai yaga duk gashin dake kansa ya juye ya zama furfura fari fat tamkar auduga! Yaje ya bama Sayyiduna Uthman bn Affan (ra) labarin abinda ya faru (Zamanin Khalifancinsa ne). Sai shi Sayyiduna Uthman din ya hana mutum ya rika yin tafiya shi ka'

MU SAN ANNABINMU (25)

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa shiryayyu. YAQIN BANU QAINUQA'A : Banu Qainuqa'a sunan wata Qabila ne daga cikin Qabilun yahudawan madeenah wadanda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya qulla alkawarin zan lafiya dasu tun farkon zuwansa garin. Nasarar da Manzon Allah (saww) ya samu a yaqin badar ta basu haushi, don haka sai suka fito fili suna bayyana qiyayyarsu ga Musulmai da kuma soyayyarsu ga mushrikan Quraishawa. Kuma sun kasance suna gadara da Qarfin tattalin arziki kasancewarsu masu sana'ar zinare ne. Suna cin mutuncin jama'ar musulmai, suna yi musu izgili har dai watarana suka yiwa wata mace musulma tsirara a kasuwarsu, ta nemi taimako awajen wani musulmi ya taimaka mata ya kashe bayahuden da ya zalunceta. Sai sauran yahudawan suka taru akansa (shi Musulmin) suka kasheshi. Wannan shine tushen yaqin. Kuma Manzon Allah (sa

RANAR RABON TAKARDU!!!

Ranar da za'ayi rabon takardu, rana ce wacce hankula ke tashi.. Idanuwa suna kuka amma babu zubar hawaye...! Mutane zasu kasance kaso uku ne awannan lokacin : # Akwai wadanda ba za'a basu littafi ba. Wato ba za'a yi musu hisabi ba. Kamar Annabawa kenan (as) da manyan Salihan bayin Allah da Siddiqai da Shahidai. # Akwai wadanda zasu karbi littafinsu ta hannun dama. Sune wadanda za'ayi musu hisabi sassauka. Wato ba za'a duba laifukansu ba. Farkon wanda zai karbi Littafinsa da hannun dama shine Sayyiduna Umar bn Khattab (rta). Kamar yadda hadisi ya fada. # Akwai wadanda zasu karbi littafinsu ta hannun haggu. Acikin wata ayar ma Allah yace zasu karba ne ta baya. Wato Mala'iku zasu sanya hannunsu na hagu su fasa musu Qirjinsu dashi, sannan su zaroshi ta baya, Sannan a miko musu littafin nasu. Za'a ce ma kowanne daga cikinsu " KARANTA LITTAFINKA DA KANKA .... " A sannan ne Dan Adam zai tuno da dukkan abinda ya aikata a rayuwarsa ta duniya.. Wat

LABARIN DAMO YANKAKKE

DAGA ZAUREN FIQHU : Wani Balaraben Qauye ya farauto Damo (alligator) ya shigo gari sai yaga Manzon Allah (saww) tare da wasu Jama'a yana yi musu wa'azi. Da yaga haka sai ya tambayi mutane "Wannan mutumin fa? wanene?". Sai akace masa "AI ANNABI NE". Saboda haka sai Balaraben Qauyen nan ya rika keta tsakanin jama'a, har sai da yazo ya tsaya agaban Manzon Allah (saww). Sannan yace: "Na rantse da lata da uzza (sunayen gumakansa ne) babu mutumin da na tsaneshi fiye da kai, Ba don kar mutanena su washeni ba, da sai na kasheka". Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) zai zare takobi ya kasheshi sai Manzon Allah (saww) ya hanashi. Balaraben Qauyen nan ya fito da damonsa (yankakke) daga cikin jakarsa, ya jefar agaban Manzon Allah (saww) sannan yace: "Na rantse da lata da uzza ba zan bada gaskiya gareka ba, har sai wannan yankakken damon yayi Imani dakai". Sai Manzon Allah (saww) yace "YA KAI DAMO!!". Sai Damon ya amsa acikin harshe

MAGANIN TSAGEWAR FATAR TAFIN HANNU DA SAURAN CIWUKAN DAJI :

TAMBAYA TA 2621 ******************* Assalamu Alaikum, Malam barka da rana ya iyali? Allah saka maku da aljanar firdaus akan taimakon dakukeyi amin. Malam yarona ne  yake  fama da kuraje a tafukan hannun shi   kurajan suna fitowane kamar bororon Wuta, wani lokaci kuma sai sufito kanana ko kuma haka kawai sai hannuwan su rinka tsagewa kamar ya yanke kuma suna Mashi kaikai Dan wani lokaci kaikain yakan hanashi bacci sosai idan kuma ya Sosa sai su rinka fitar da jini.Malam dan  Allah ataimaka mana, daga  dalibarku. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullah. Irin wadannan chutukan fata ne kuma basu rasa alaqah da ciwon daji irin na fata. Amma ga wasu abubuwa nan ki jarrabah. 1. Ki samu lalle (irin wanda kuke yin Qunshi dashi) ki kwaba da ruwa amma ki sanya man zaitun kamar cokali guda aciki. Sai kiyi masa Qunshi a hannayen nasa. Lalle yana maganin mafiya yawan ciwukan fata. Kici gaba da yi masa Qunshin duk bayan sati biyu. In shaAllah cikin Qankanin lokaci Qirajen zasu dena fitow

MADUBIN DUBAWA (70)

Yau madubin namu zai waiga baya ne ya dauko mana wani abu daga rayuwar magabatanmu wato tabi'ai da tabi'ut tabi'un. Daga cikin magabata akwai wadanda tsoron wutar lahira da kuma tunaninta yasa suka haramta wa kansu yin dariya anan gidan duniya. Isma'eel As-Suddiy (rah) yace "Lokacin da Hajjaju bn Yusuf (wani azzalumin gwamna ne) yasa aka kamo masa babban Malamin tabi'ai din nan mai suna Sa'eed bn Jubair kafin ya kasheshi sai ya tambayeshi cewa "Labari ya sameni cewa wai kai baka ta'ba yin dariya ba tunda kake!". Sai Sa'eed bn Jubair (rah) yace masa "Ta yaya zan rika dariya alhali an riga an hura jahannama, Kuma Qukuman cikinta an riga an kakkafasu, Kuma Zabaniyawan cikinta an riga an tanadesu ? (Qukumi shine irin chain din da ake Qakaba musu a wuyansu lokacin da ake jibgarsu ana azabtar dasu. Zabaniyawa kuma sunan Mala'ikun nan ne Qarfafa guda goma sha tara wadanda Allah ya tanadar dasu domin azabtar da 'yan wuta). Bayan H

MU SAN ANNABINMU (24)

Da Sunan Allah Mai Girma, salati da amincinsa su tabbata bisa bawansa mafi girma, Annabinmu Muhammadu tare da Iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu girma. YAKOKIN ANNABI (SAWW) : Yakokin da Manzon Allah (saww) yayi azamaninsa, ba wai yana yinsu ne domin daukar fansa ko son zubar da jini ba. A'a yakokin nasa sun kasance ne domin mayar da kaidin abokan gaba da ladabtarwa ga duk wani mai ta'addanci, da kuma kira zuwa ga addinin Allah. Annabi (saww) yayi yakoki da dama kafin badar da kuma bayanta, domin amintar da garin Madeenah da kuma bayar da kariya gareta daga hare-haren kafirai. Akwai yakokin da ya samu halarta, sun kai kamar guda ashirun da bakwai ko da takwas. Akwai kuma wasu da dama wadanda bai je ba amma ya tura da rundunoni karkashin jagorancin amintattu daga cikin Sahabbansa. YAQIN BADAR : Manzon Allah (saww) ya samu labarin gabatowar wani ayarin fatauci na Quraishawa mai kunshe da rakuma dubu dauke da kayan fatauci, Kuma Abu Sufyan ne yake jagorantar tafiyar

MU SAN ANNABINMU (12)

Da sunan Allah Makadaici, Salati da aminci su tabbata ga Annabinmu tare da iylan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyan bayansu da kyutatawa. Wannan shine ci gaban darasinmu na Zauren Fiqhu wanda acikinsa muke kawo muhimman lamura acikin tarihin Ma'aikinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). ZAMANSA A KOGON HIRA'U ***************************** Annabi (saww) ya kasance akowacce shekara yakan kebance kansa tsawon wata guda ya tafi kogon hira'u wanda ke kan Jabalun Nur ya zauna yana tunani cikin lamarin Ubangijinsa kuma yana ibadah (bautar Allah) bisa addinin Kakansa Annabi Ibrahim (alaihis salam). Wannan tun kafin ya cika shekaru arba'in aduniya kenan. Amma bayan ya cika 'dan shekara arba'in aduniya watarana yana zaune acikin kogon sai ya hangi siffar wata Halitta mai girman gaske ta cika dukkan sasanni. Ashe Shugaban Mala'iku ne wato Jibreelu (amincin Allah ya tabbata gareshi). Yazo ya rungumeshi zuwa jikinsa runguma mai tsanani sannan y

ILLOLIN SHAN TABAR WEEWI

Acikin 'yan shekarun nan da matasa suka lalata kansu ta hanyar amfani da miyagun kwayoyi, Tabar Weewi ita ce kan gaba fiye da dukkan miyagun Kwayoyin da matasan suke amfani dasu. Wannan yasa ZAUREN FIQHU ya gudanar da bincike akanta domin ganowa irin illolinta, da kuma yadda take aiki wajen ruguza lafiyar jikin masu ta'ammali da ita. SUNAYENTA ************* Kasancewar ana amfani da ita kusan adukkan nahiyoyin duniya, wannan yasa Tabar Weewi take da sunaye kala-kala kamar haka: WEEWI, Ganye, Marijuana, Indian Hemp, Ganja, Pot, Igbo, Weed, Canabees, Hasheesh, Texas Tea, da dai sauransu. ILLOLINTA *********** Ganyen tabar WEEWI yana kunshe da Sinadarai sama da guda Arba'in masu chutar da lafiyar 'Dan Adam. Daga cikinsu har da sinadarin TETRA-HYDRO-CANNABINOL (T.H.C.) wani mummunan sinadari ne wanda yake chanza ma kwakwalwar 'Dan Adam yanayin yadda take karbar sakonni da yadda take sarrafa su. Duk lokacin da mashayin Weewi ya Zuki hayakinta, shi wannan Mummunan

HANYOYIN KANKARAR ZUNUBAI (1)

TUBA DAGA DUKKAN ZUNUBAI Daliban Zauren Fiqhu da sauran jama'ar musulmai, Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Wannan sabon jerin karatu ne wanda yake kunshe da wasu hanyoyin samun kankarar zunubai da lada mai yawa. Zai  rika zuwa muku tare da ayoyi da hadisai ingantattu. In shaAllah. Hanya ta farko wacce zaka bi amatsayinka na bawan Allah domin neman kusanci da mahaliccinka ita ce hanyar tuba daga duk wani zunubi da kasan kana aikatawa, Qananan zunubai da manyansu in dai ka tuba domin Allah, to zai karbi tubanka cikin karamcinsa kuma ya gafarta maka laifukanka. Ya fa'da acikin littafinsa mai girma yace : "KU TUBA ZUWA GA ALLAH BAKI DAYANKU YA KU MUMINAI, TSAMMANIN TABBAS ZAKU RABAUTA". Suratun Nur ayah ta 31. Kuma kada girman zunubanka ko kallon yawan laifukanka, ko laifukanki ya hanaka, ko ya hanaki tuba. Hakika babu abinda yake gagarar Ubangiji. Kada ku manta fa Allah yayi kira garemu ta hanyar Annabinsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam)

FA'IDODIN TSAMIYA DAGA ZAUREN FIQHU

Tsamiya wata bishiya ce wacce ake shukata kuma ana magani da ita tun kusan shekaru dubu uku da suka gaba. Kuma ana samunta acikin dazuzzukan nahiyarmu ta Afirka da kuma kudancin nahiyar Asia. Likitocin Musulunci sun dade suna amfani da 'ya'yan bishiyar domin magance larurori masu yawa, haka kuma ana amfani da ita wajen hada nau'o'in abinci da abinsha. 'Ya'yan wannan bishiya ta tsamiya suna kunshe da sinadarai masu yawa sosai wadanda ke Qara ma jikin Dan Adam amfani mai yawa.  Misali : - Vitamin A 151, Vitamin E, Vitamin B da kuma C. Sannan acikinta akwai Calcium, Potassium, thiamine, Tartaric Acid, Phosphorous, Proteins, Magnesium, Riboflavin. Haka kuma sabobbin ganyenta suna kunshe da sinadarin Sulfur da Calcium mai yawan gaske. Yanzu ga wasu fa'idodi ka'dan daga cikin dimbin abubuwan amfani dake cikin tsamiya : 1. CIWON ZUCIYA : Shan kunun tsamiya ko farau-farau (Juice) wanda aka yishi da tsamiya zai iya zama riga-kafi daga kamuwa da chutar hawan

MU SAN ANNABINMU (11)

Da sunan Allah Mamallakin komai da kowa, Salatinsa da amincinsa su tabbata ga Mabudin alkhairansa, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya. SABUNTA GININ KA'ABAH ************************* Yayin da shekarun Manzon Allah (saww) suka cika talatin da biyar aduniya, anyi wani ruwa mai yawa acikin garin Makkah wanda ta sanadiyyar ambaliyarsa ya kwararo ya cika dakin Allah mai alfarma (KA'ABAH) har sai da bangwayenta suka tsattsage. Saboda tsoron rushewarta sai Quraishawa suka yanke shawara atsakaninsu cewa zasu rushe ginin sannan su sake mayar dashi kamar yadda yake. Tare da bayar da gudunmuwa daga mafi tsarkin dukiyarsu, sunyi nasarar mayar da ginin. To amma yayin da aka zo wajen mayar da Baqin dutsen nan (Hajarul Aswad) wanda ke maqale ajikin dakin Ka'abah, sai suka samu sa'bani atsakaninsu akan shin wanene zai dauki dutsen ya sanyashi awajensa, saboda alfahari da girman dake cikin wannan. Daga karshe sai suka yanke shawarar cewa du

MU SAN ANNABINMU (10)

Da Sunan Allah Masanin fili da boye, Salati da aminci su tabbata ga Ma'abocin Alqur'ani da Sab'ul Mathaniy, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da matayensa da dukkan Sahabbansa da Salihan bayin Allah baki dayansu. AURENSA DA NANA KHADIJAH (RA). Manzonmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) tyn tasowarsa ya shahara da kyawawan halaye da dabi'u irin su gaskiya da rikon amana da hakuri da kyautatawa, da dukkan wasu halayen ababen yabawa. Ita kuma Nana Khadijah bintu Khuwailid (ra) wata Mace ce Ma'abociyar kyawu da daukakar nasaba ga kuma dukiya mai yawa wacce Allah ya bata a hannunta. Ta kasance tana bayarwa ana yi mata kasuwanci da dukiyarta ta hanyar aika Mazaje zuwa garuruwa masu nisa domin saye da sayarwa sannan a raba ribar da aka samu. To Nana Khadijah watarana ta gani acikin mafarkinta cewa rana ta sauko daga sama ta fa'do acikin dakinta, akan Qirjinta. Yayin da ta farka afirgice ta gaya ma wani Malami makarancin Attaura kuma 'Dan Baffant

MU SAN ANNABINMU (02)

MAHAIFANSA : Mahaifinsa shine Abdullahi 'dan AbdulMuttalibi 'dan Hashim. Yana daga mafiya kyawu da nagartar samarin zamaninsa. Mahaifiyarsa kuwa ita ce Nana Ãminatu (Az-Zuhriyyah) 'yar Wahbin 'dan Abdu Manaf 'dan Zuhrata. Ta fito daga dangi masu tsarki da nagarta da daukaka daga cikin dangogin larabawa Quraishawa. HAIHUWARSA : An haifi Shugabanmu Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ne a garin Makkah acikin unguwar banu Hashim, ranar litinin sha biyu (12) ga watan rabee'ul awwal ashekarar giwaye, wacce tazo daidai da 20 ga watana aprilu shekara ta 571 miladiyyah. An haifeshi ne maraya kasancewar mahaifinsa ya riga ya rasu tun yana da 'yan watanni acikin mahaifiyarsa. Kuma an haifeshi mai tsarki mai haske mai Qamshi, idonsa da tozali. Kuma ya sauka tare da haske mai girma wanda ya haskake garin makkah baki dayansa har garuruwa masu nisa. Kakansa Abdul Muttalibi ne ya ra'da masa wannan suna "MUHAMMADU" bisa ilhamar Ubang

MU SAN ANNABINMU (04)

Godiya ta tabbata ga Allah Mamallakin zukata da hankula, wanda ya zabi zukatan wasu daga cikin bayinsa kuma ya karkatar da zukatansu zuwa ga shagaltuwa da kokarin sani da koyi da neman cikar soyayyar Manzonsa wanda ya aiko zuwa ga dukkan halittu (saww). Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da bai ta'ba magana bisa son rai ba, fache bisa wahayi daga Ubangijinsa. TSAGAWAR KIRJINSA : Kamar yadda muka ta'ba bayani acikin wani darasinmu na Zauren Fiqhu Whatsapp, an tsaga Kirjin Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ne har sau hudu alokuta daban daban. Kuma ga takaitaccen bayanin yadda kowanne ya faru : NA FARKO : Lokacin da ya cika shekaru hudu aduniya, sai Ubangijinsa (SWT) ya turo masa Mala'iku guda biyu wato Jibreelu da Meeka'ilu (amincin Allah ya tabbata garesu). Suka zo suka tarar dashi alokacin yana kiwon tumakin Halimatus Sa'adiyyah tare da sauran yaranta. Mala'ikun nan suka kwantar dashi suka tsaga qirjinsa suka fito da zuciyarsa madau

MU SAN ANNABINMU (04)

Godiya ta tabbata ga Allah Mamallakin zukata da hankula, wanda ya zabi zukatan wasu daga cikin bayinsa kuma ya karkatar da zukatansu zuwa ga shagaltuwa da kokarin sani da koyi da neman cikar soyayyar Manzonsa wanda ya aiko zuwa ga dukkan halittu (saww). Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da bai ta'ba magana bisa son rai ba, fache bisa wahayi daga Ubangijinsa. TSAGAWAR KIRJINSA : Kamar yadda muka ta'ba bayani acikin wani darasinmu na Zauren Fiqhu Whatsapp, an tsaga Kirjin Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ne har sau hudu alokuta daban daban. Kuma ga takaitaccen bayanin yadda kowanne ya faru : NA FARKO : Lokacin da ya cika shekaru hudu aduniya, sai Ubangijinsa (SWT) ya turo masa Mala'iku guda biyu wato Jibreelu da Meeka'ilu (amincin Allah ya tabbata garesu). Suka zo suka tarar dashi alokacin yana kiwon tumakin Halimatus Sa'adiyyah tare da sauran yaranta. Mala'ikun nan suka kwantar dashi suka tsaga qirjinsa suka fito da zuciyarsa madau

MU SAN ANNABINMU (03)

Da sunan Allah Makadaici, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayyen Halittu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da dukkan bayin Allah Salihai. SHAYARWARSA (SAWW)  : Farkon wacce ta shayar dashi aduniya ita ce mahaifiyarsa Nana Aminatu 'yar Wahb, daga nan sai wata baiwar baffansa Abu Lahab wacce ake kira Thuwaibatul Aslamiyyah (rta) ta shayar dashi itama. Kuma dama Abu Lahab din ya 'yantar da ita tun bayan haihuwar Manzon Allah (saww) alokacin da tazo yin albishiri gareshi cewa Matar 'dan uwansa ta haifi 'da namiji. Sai kuma Haleematus Sa'adiyyah itama ta shayar dashi. Kuma ta dalilin wannan shayarwar ta samu daukaka da fifiko da yalwar arziki. Gidanta ya cika da albarka da arziki da ni'ima saboda albarkacin kasancewar Annabi (saww) tare da ita. Kuma yana daga cikin girmamawar da Allah yayi masa, dukkan matayen da suka shayar dashi sun karbi addininsa (saww). Koda yake akwai riwayar da tazo da akasin haka, amma riwayar musuluntar tasu tafi Qarfi kuma gareta